Za’a Saka Fasahar 5G a Najeriya a 2022 – Farfesa Pantami

 

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, yace za’a saka fasahar 5G a Najeriya a watan Janairu, 2022.

Ministan yace fasahar 5G zata taimaka matuƙa gaya wajen kare manyan kayan gwamnati, da kuma cafke masu lalata su.

Pantami ya faɗi haka ne a Maiduguri, a wurin taron da ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu ta shirya kan lalata hanyoyin sadarwa da hasken wutar lantarki.

Abuja – Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, yace za’a saka fasahar 5G a Najeriya a watan Janairu, 2022, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Ministan ya bayyana cewa fasahar ta 5G zata taimaka matuƙa gaya wajen rage aikata manyan laifuka na lalata kayayyakin gwamnati.

Pantami ya faɗi haka ne a Maiduguri, ranar Alhamis, a wurin taron da ma’aikatar yaɗa labarai ta shirya kan lalata kayan ɓangaren sadarwa da wutar lantarki.

Ministan, wanda daraktan fasaha na hukumar sadarwa (NCC), Ubale Maska, ya wakilta, yace ba da jimawa ba majalisar zartarwa ta ƙasa ta amice da sanya fasahar 5G a Najeriya.

Wane amfani fasahar 5G zata yi a Najeriya?

Bugu da ƙari, ministan yace fasahar zata taimaka wajen ƙara kulawa da yan ta’adda dake lalata manyan kayayyakin gwamnati a faɗin ƙasa, domin za’a ɗauki matakin kame su da fasahar.

Ya kuma bayyana cewa akwai sashin yanar gizo na sadarwa 50,000 a faɗin Najeriya, kuma saka fasahar zai taimaka sosai wajen amfani da su.

Yace:

“Kamfanonin sadarwa na MTN, Glo, Airtel da kuma 9Mobile sun faɗa mana cewa an samu rahoton matsalar ɗaukewar sabis dubu 16,000 daga watan Janairu, 2021, zuwa Yuli, 2021 a faɗin Najeriya.”

A cewar ministan, an samu waɗannan matsalolin ne saboda datse sabis, rashin karfi da kuma sace wasu muhimman kayayyaki,wanda ke jawo lalacewar sabis a yankunan, kamar yadda Punch ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here