Nan ba da Jimawa ba Man Fetur ɗinmu zai Shiga Kasuwa – Dangote
Mai kamfanin Matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote ya sanar da cewa da
zarar kamfaninsa ya kammala wasu muhimman abubuwa da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), man fetur ɗin kamfanin nasa zai shiga kasuwa.
Hamshakin ɗan kasuwar ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Talata, biyo bayan kaddamar da kason farko na man daga matatar kamfanin mai ganga 650,000 a kowace rana.
Dangote ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za su iya sa ran samun man fetur mai inganci da daɗewa
Read Also:
“Ba za ku ƙara fuskantar matsalolin da injinan motoci ke baku ba,” in ji Dangote.
“Man fetur ɗin mu zai yi daidai da na kowace ƙasa a duniya; babu wanda zai wuce mu ta fuskar inganci,” in ji shi.
Dangote ya jaddada fa’idar tattalin arzikin da ayyukan matatar kamfanin ke da su, inda ya bayyana cewa za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a Najeriya tare da daidaita darajar naira da kuma taimakawa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa,” in ji shi.
Matatar mai ta Dangote da ke Legas ta dala biliyan 20, ta fara aiki a watan Disambar da ya gabata.