FG na Barazanar Maka ASUU a Kotu
Gwamnatin tarayya ta ce idan har bata da wani zabi za ta iya maka kungiyar malaman jami’a ASUU a kotu kan yajin aiki.
Ministan Kwadago da Ayyuka, Chirs Ngige ne ya yi wannan barazanar a karshen taron da suka gudanar da malaman a ranar Laraba yayin zantawa da manema labarai.
Read Also:
An dai dade ana ta yin tarurruka tsakanin gwamnatin da kungiyar malaman kan yajin aikin da suke yi na tsawon watanni bakwai amma har yanzu ba a cimma matsaya ba Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi barazanar shigar da kungiyar malaman jami’ar Najeriya, ASUU, kara a kotun ma’aikata kan yajin aikin da ta ke yi da ya-ƙi-ci-yaƙi-cinyewa kamar yadda TVC ta ruwaito.
Ministan Kwadago da Ayyuka, Dakta Chris Ngige ne ya yi wannan barazanar a karshen taron da suka yi na tsawon kimanin awa uku da shugbannin kungiyar a Abuja.
Kamar yadda suka saba, bangarorin biyu sun bayyana fatar ganin an kawo karshen yajin aikin a jawabinsu na bude taron. Amma bayan kimanin awa biyu cikin taron, ASUU ta ce har yanzu babu wani sabon abu da aka gabatar mata.
A hirar da ya yi da manema labarai, Ministan ya ce akwai yiwuwar gwamnati ta dauki matakin shari’a kan malaman jami’ar da ke yajin aiki don kawo karshen rashin jituwar.