Yanda Zaɓen Amurka Ya Juya Zuwa zanga-Zanga 

Magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar Republican, Donald Trump sun yi zanga-zanga a Arizona.

Masu zanga-zangar sun yi wa ofishin ƙidaya na jihar zobe ɗauke da rubutu da ke nuna ƙin amincewarsu da ƙidayar.

Wasu daga cikinsu suna ta maganganu da ke iƙirarin cewa ƴan Democrats suna tafka maguɗi wurin ƙidayar Magoya bayan shugaban Amurka, Donald Trump, cikinsu ana zargin wasu na ɗauke da bindigu, sun zagaye ofishin zaɓe na Maricopa County da ke Arizona suna zanga-zanga kan zabe.

Wani bidiyo da aka nuna a CNN, ya nuna magoya bayan Trump ɗauke da saƙonni da ke nuna rashin jin daɗinsu kan hasashen da ke nuna jam’iyyar Democrats za ta yi nasarar cin kwallejin zaɓe 11 a jihar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Joe Biden wadda shine ɗan takarar jam’iyyar Democrat shine a kan gaba a Arizona duk da cewa tazarar ba yawa.

Kwamitin yaƙin neman zaɓe na Trump a daren ranar zaɓe sunyi watsi da rahotannin cewa sun sha kaye a jihar inda suka ce akwai ƙuri’u na wasiƙa da ba a ƙirga ba tukuna.

“Wane ke duba ƙuri’un wasika?” Kamar yadda aka jiyo wani mai zanga zanga na tambaya da na’urar amsa kuwwa a wani bidiyo da wakilin BBC Gadi Schwartz ya wallafa a Twitter. “Democrats ne,” a cewar amsar da wata mata ta bada. “Democrats ne ke duba su.”

A halin yanzu Biden ya bawa Trump tazara da kimanin ƙuri’u 80,000 a jihar kamar yadda The Associated Press ta ruwaito.

A daren Laraba, jihar ta ƙidaya ƙuri’u fiye da 300,000 a cewar rahoton Washington Post. Tuni dai Trump ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta inda ya ke iƙirarin cewa Democrats ne satar ƙuri’u.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here