Gwamna Mutfwang ya Sanar da Haramta Kiwo da Daddare a Fadin Jihar Filato
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar.
A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan ta’addanci” da ke da nufin tarwatsa mazauna yankin da kuma tauye hakkinsu na kasancewa cikin lumana a yankunansu.
Gwamnan ya kuma haramta safarar shanu cikin ababen hawa bayan karfe 7 na dare.
Ya kuma hana amfani da babura daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a faɗin jihar har na wani tsawon lokaci inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take.
Read Also:
Ya ce ” Ina jinjinawa masu ba da agajin gaggawa da jami’an tsaro bisa gaggarumin matakin da suka ɗauka, ina kuma gode wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar da adalci cikin gaggawa.”
Muftwang ya ce dole ne al’ummomi su ba da himma wajen kare kansu a cikin iyakokin da doka ta tanada.
Ya ce ”Ina kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin matasa da su sake farfaɗo da sintiri tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. Dole ne mu haɗa kai don kare ƙasarmu, domin tabbatar adalci yayin da mu ke la’akari da kiyaye dokokin ƙasa.”
Aƙalla mutane 50 ne rahotanni suka ce an kashe bayan wasu ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Kimakpa da ke gundumar Miango a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar a ranar 14 ga watan Afrilu.
Harin ya zo ne makonni biyu kacal bayan da wasu ƴan bindiga suka kashe mazauna ƙauyuka biyar a ƙananan hukumomin Bokkos da Mangu.
Hukumomin ƙasar dai na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun daƙile hare-hare a jihar da aka daɗe ana fama da rikicin kabilanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.