Squid Game: fim ɗin da Aka Kalla Sau Miliyan 111 a kwana 28
Ba a bar ƴan Najeriya a baya ba wajen tattaunawa kan fim mai dogon zango da ya shahara a duniya a baya-bayan nan wanda kamfanin Netflix ya samar wato Squid Game.
Mutane sun karaɗe shafukan sada zumunta da muahwara na ƙasar da batun fim ɗin, kamar dai yadda takwarorinsu a ƙasashen duniya ma ke yi.
A shafin Facebook a Najeriya bayanai sun nuna an yi maganar fim ɗin sau kusan da 150,000 a ƴan kwanakin nan.
A shafin Instagram kuma bayanan sun nuna a fadin dunyiya an yi amfanid a maudu’in #squidgame sau 732,183.
Duk an san da fitowar fim ɗin, amma a yanzu ya tabbata a hukumance: Squid Game ya zami shi ne gagrumin fim mai dogon zango da kamfanin Netflix ya taɓa ƙaddamarwa.
An kalli diramar ta ƙasar Koriya sau miliyan 111 a kwanaki 28 na farko inda ya doke shirin Bridgerton da a yake kan gaba da miliyan 82.
An lissafa yawan waɗanda suka kalli fim ɗin ne ga duk wanda ya kalli minti biyun farko.
Mataimakin shugaban Netflix na Koriya da Kudu maso gabashin Asiya da Australiya da New Zealand ya ce shirin ya samu gagarumar nasara “fiye da zatonmu.”
Minyoung Kim ya shaida wa CNN cewa: A lokacin da muka fara zuba jari kan shirye-shirye da fina-finan Koriya a 2015, mun san cewa so muke mu yi abin da zai jawo hankalin mutane a yankin Koriya da Asiya da ma duniya baki ɗaya.
“A yau, fim din Squid Game ya zama gagara gasa fiye da mafarkinmu.”
Shirin mai zango tara, wanda aka fara a watan Satumba, yana ba da labarin wata ƙungiyar wasu ƴan bana bakwai ne suke yin irin wasannin yara wato games.
Akwai kyauta ta dala biliyan 45.6 da aka sanya ga wanda ya ci, wadda ba za ka ji haushin rasa kyautar ba sai lokacin da ka faɗi a wasan kuma aka kashe ka.
Kowa magana yake a kan fim din Squid Game kama daga kan fitattun mutane zuwa mashahuran ƴan ƙwallo.
Tarurarin cikin fim ɗin sun yi suna a duniya – Jung Ho-yeon wanda ya fito a matsayin Sae-byeok ya samu mabiya miliyan 14 a Instagram tun bayan ƙddamar da shirin ranar 17 ga watan Satumba, kamar yadda mujallar Forbes ta ce.
To ko mene ne sirrin nasarar fim ɗin?
Me ya sa Squid Game ya baza duniya?
Kamar dai wasu abubuwan da suka faru a fim ɗin The Hunger Games,, ko fim ɗin Battle Royale da aka yi a shekarar 2000, shirin ya mayar da hankali ne a kan ƙungiyar wasu mutane a Koriya Ta Kudu da bashi ya yi wa katutu.
Da fari an yaudare su ne (sai kuma suka so yin na sa kai) kan yin wani wasan yara ,mai haɗari, da suka fahimci hakan zai iya zama damarsu kaɗai ta lashe kyautar kuɗin da suke buƙata don su rayu.
Arif Sani wani matashi ne da yake bibiyar shirin a Najeriya, ya kuma ce wa BBC “hikimar da aka yi amfani da ita, da yadda mutane ba tare da bincike kan yadda abin yake ba suka shiga abin da zai kai su ga hallaka, su ne abubuwan da suka fi jan hankalina dangane da fim ɗin.”
Chloe Henry wata masoyiyar fim ɗin ce, kuma ta ce Squid Game ya fita daban da sauran.
“Wani abu ne da ba a taɓa yin irinsa ba a baya,” a cewar matar mai shekeara 26 daga Sheffield, kamar yadda ya shaida wa shirin Radio 1 Newsbeat na BBC.
“A sauran fina-finai kana iya gane me zai faru a karshe, amma wannan abin sha’awa ba ka isa ka canka ba – don abin da ba ka taɓa zata ba na iya faruwa.”
A ganinta taurarin fim ɗin da yanayin yadda abubuwa ke tafiya kawai zai iya jan hankalinka da fim ɗin.
“Yanayin yadda Seong Gi-hun ke nuna komai kamar a zahiri a fim din yana burge ta kuma yana sa ta ji daɗin kallon.”
Seong Gi-hun yana son yin caca sosai kuma bashi ya yi masa katutu har yana fuskantar barazanar rasa ƴarsa. Shi ne fitaccen jarumi a shirin.
Chloe ta kuma ce fim din na nuna wa masu kallo damar ganin Koriya Ta Arewa ta fuskoki daban-daban.
“Mutane na tunanin Koriya Ta Arewa babbar ƙasa ce da take da ɗumbin masu arziki, don haka abin ƙayatarwa ne da na ga wasu abubuwa da ba a maganarsu a kan ƙasar, kamar fafutukar rayuwa da talauci.”
Kamar yadda Koriya ta sake yin fice sosai a Birtaniya saboda fim ɗin, haka ma ƙaunar ƙasar ta fara yin katutu a zuciyar ƴan Najeriya.
Mutane a Birtaniya sun yi ta bincike kan batutuwan da suka shafi Koriya a watan Oktoba fiye da ko yaushe, kamar yadda bayanan Google Trend suka nuna, kuma a watan da ya gabata ƙamus ɗin Oxford English Dictionary ya ƙara sabbin kalmomi 26 da suka samo asali daga Koriya.
Sannan a Najeriya ma Squid Game na daga cikin abin da mutane suka fi neman ƙarin bayani a kansa a Google.
Dr Hye-Kyung Lee – wani da ke bincike kan yadda fina-finan Koriya ke tasiri a Kwalejin Kings ta Landan ya ce, “wahalar da aka nuna ana sha a fim ɗin Squid Game ita ce abin da ya sa fim ɗin ke jan hankalin mutane a fadin duniya.
“Waɗannan shirye-shiryen suna nishaɗantarwa kuma suna da kamanceceniya da ka iya jan hankalin mutane a faɗin duniya.
“Suna nuna yanayin zamantakewar mutane da tattalin arzikinsu, waɗanda mutane za su ga tamkar abin da ke faruwa da su ne a zahiri.”
Dr Lee ya ce fina-finan Koriya kan taɓo batutuwan da suka shafi tattalin arziki da siyasa, amma Squid Game ya taɓo fiye da abin da ya fi haka.
“Saƙon ya kai ƙololuwa kuma ya yi daidai da abin da ke faruwa yanzu.”
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here