Firaiministan Haita ya yi Murabus

 

Firaiministan Haiti, Ariel Henry ya yi murabus sakamakon matsin lamba na kwanaki da kuma karuwar tashin hankali a kasar.

Hakan na zuwa bayan da shugabannin ƙasashen yankin Karibiyan suka gana a Jamaica domin tattauna halin da ake ciki a Haiti.

Mista Henry ya kasa komawa gida saboda barazanar ƙungiyoyin ƴan daba, wadanda suka mamaye babban birnin ƙasar kuma a yanzu haka yana samun mafaka a kasar Puerto Rico.

A wani jawabi da ya gabatar ta bidiyo, Mista Henry ya buƙaci ƴan ƙasar ta Haiti su kwantar da hankalinsu.

“Na yi murabus ba tare da ɓata lokaci ba kuma za a naɗa gwamnatin riƙon ƙwarya,” in ji Mista Henry.

Henry, wanda ya jagoranci ƙasar na rikon ƙwarya tun daga watan Yulin 2021 bayan kashe tsohon shugaban kasar Jovenel Moïse, ya jinkirta zaɓe sau da dama inda ya ce sai tsaro ya inginta kafin a yi zaɓen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here