Tsananin Zafi: Johannesburg na Fama da ƙarancin Ruwan Sha

 

A birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, mahukunta sun ɗora laifin ƙarancin ruwa da ake fuskanta a birnin kan tsananin zafin da ake fama da shi, lamarin da ya sa magudanan ruwa suka bushe a wasu sassan birnin na tsawon makonni.

Hukumar Kula da Yanayi ta Afirka ta Kudu ta yi gargaɗi a jiya Litinin kan tsananin zafi da ya wuce kima.

Hukumar samar da ruwan sha ta gwamnati ta ce karuwar yawan ruwan da mutane ke amfani da shi da kuma ƙafewar wuraren tara ruwa na ƙara ta’azzara matsalar.

Ƙarancin ruwa ya zama ruwan dare a Johannesburg, kuma ya haifar da zanga-zanga a baya.

Matsalar ruwan da ake fama da ita a halin yanzu ta fara ne a karshen shekarar da ta gabata amma ta kara ƙamari a ‘yan makonnin nan.

Katsewar ruwan ba gidaje kadai ya shafa ba har ma da ma’aikatun gwamnati.

A makon da ya gabata, gidaje da dama ciki har da asibitoci, an tilasta musu sayen ruwa daga tankunan ruwa bayan da tsawa ta lalata wata babbar tashar tace ruwa, lamarin da ya janyo katsewar samar da ruwan sha na tsawon kwanaki.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here