Yawancin Kuɗaɗen da CBN,Emefiele ya Fitar ba Tare da sa Hannun Buhari ba – Ngelale

 

Fadar shugaban Najeriya ta ce yawancin kuɗaɗen da aka fitar daga Babban bankin ƙasar (CBN) ƙarƙashin shugabancin Godwin Emefiele, an fitar da su ne ba tare da sa hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba.

Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi a shirin With Chude na Chude Jideonwo wanda aka watsa a gidan talabijin na Channels.

Ngelale ya ce dole ne gwamnatin da ta gabata ta ɗauki alhakin wasu abubuwan da suka faru a babban bankin ƙarƙashin jagorancin Emefiele.

Ngelale ya jaddada cewa, yayin da Buhari ya samu nasarori a wasu fannonin samar da ababen more rayuwa, rashin sanya ido kan al’amuran Babban bankin ya taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar.

Duk da cewa ya amince cewar Bola Tinubu ya bai wa gwamnati tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari goyon baya, Ngelale ya ce a yanzu Tinubu na ƙoƙarin ganin ya magance matsalolin da suka haifar da taɓarɓarewar tattalin arzikin kasar da ta faru a zamanin gwamnatin Buhari.

Ngelale ya yi nuni da cewa Buhari ne ya yanke shawara dangane da tsawaita wa’adin mulkin Emefiele, duk kuwa da cewa shugaban bai san al’amuran da ke gudana a Babban Bankin ba.

Ngelale ya bayar da misali da yadda Babban Bankin ya fitar da kuɗi dalar Amurka miliyan 6.2 ga masu sa ido kan zaɓuka daga ƙasashen waje, wanda aka ce da sa hannun Buhari ne, inda daga baya aka yi zargin jabu ne.

Emefiele, wanda shugaban kasa Goodluck Jonathan ya naɗa tun farko, ya ci gaba da zama gwamnan CBN a gwamnatin Buhari.

Sai dai kuma ya fuskanci shari’a a watan Yunin da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa da suka hada da na sa hannun bogi da kuma karbar kudi ta hanyar ƙarya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here