Firaministan Pakistan na Fuskantar Gagarumin Kalubale na Harkar Siyasarsa

Firaministan Pakistan Imran Khan na fuskantar gagarumin kalubale na harkar siyasarsa, bayan da ‘yan adawa ke neman tsige shi daga kan mulki a wata kuri’a nuna rashin amincewa.

‘Yan majalisar dokokin kasar za su sawo bakin aiki a ranar Alhamis su fara tafka muhawara, a yayin da makomar Mista Khan kenuna alamun sukurkucewa. An sa ran kada kuri’ar a ranar Litinin.

A cikin kwanakin baya akwai hada hada da dama – kuma abinda wa suke cewa wasu dabaru ne da aka yi amfani da su daga cikin littafin nan na wasan kwaikwayo na Machiavelli – da ya haddasa wa aminan Khan da dama suka juya wa jam’iyarsa ta Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) baya.

Mafi rinjayen kujeru 172 cikin kujerun ‘yan majalisar dokoki 342 za su gajarce wa’dain mulkinsa a matasyin firaminista.

Imran Khan, wanda aka zaba a cikin watan Yulin shekarar 2018, yin alkawarin shawo kan matsalar cin hanci da rashawa da kuma gyara tattalin arziki, bai tafi yadda ya kamata ba.

A ranar Lahadi ne ya karbi bakuncin wani gagarumin gangami a birnin Islamabad don nuna cewa har yanzu yana da tagomashin magoya bayansa.

Yayin da yake ta suka da kakkausar murya kan abokan hamayyarsa – firaminstan wa’adi uku Nawaz Sharif da Asif Zardari, mijin firaminista Benazir Bhutto da aka yi wa kisan gilla.

Mista Khan ya kuma aika da wata wasika ga taron jama’ar yana mai zargin cewa ta kunshi shaidar ” hadin bakin kasashen waje” tare da ”barayi masu cin hanci da rashawa”.

Har yanzu bai bayyana abubuwan da wasikar ta kunsa ba, duk da alkawuran da ya sha yi.

Har ila yau wani karin rudanin, an dage jawabinsa ga kasa a ranar Laraba ba tare da wani bayani ba.

Raba hannun riga da sojoji?

Gwamnatin Imran Khan ba ta bukatar dubawa da nisa kafin a gano matsalolinta.

Ta rasa goyon bayan jama’a kan matsalar hauhawar farashin kayyaki da kuma tarin basussukan kasashen waje.

“Misali, daga watan Janairun shekarar 2020 zuwa Maris din shekarar 2022, hauhawar farashin kayyaki a kasar India ya kasance kashi 7 bisa dari ne, a yayin da na Pakistan kashi 23 bisa dari,” in ji Uzair Younus, daraktan hukumar Pakistan Initiative mai mazauni a Washington.

Amma kuma karuwar tsamin dangantaka da sojojin – kamar yadda masu gyara masa hanyoyin samun nasarar siyasarsa ke dauka, duk da cewa duka bangarorin biyu sun musanta haan – shi ne dalilin da ya sa masu sharhi amanna cewa komai a bayyane yake a gare shi.

Ga masu sa ido da dama, za a iya duba musabbabin takaddamar da ke faruwa tun daga baya a watan Oktoba lokacin da Mista Khan ya ƙi amincewa ya rattaba hannu kan takardar bayar da muƙami wa sabon shugaban hukumar leken asiri mafi girma a kasar Pakistan ISI.

Mai sharhi Arifa Noor ya yi amanna cewa a Pakistan takaddama tabbatacciya ce a dangantakar da ke tsakanin fararen hula da sojoji – da kai tsaye suka mulki kasar na kusan tsawon lokaci – batun maye gurbin shugaban hukumar leken asirin Janar Faiz Hameed ya haddasa tsamin dangantaka.

Mai bincike kuma mazaunin kasar Abdul Basit ya amince cewa takun sakar na faruwa ne saboda ”girman kan” Mista Khan da kuma ”taurin kai’ wanda ya haddasa matsalolin suka fita a bainar jama’a da a ko da yaushe aka fi tattaunawa a boye.

“Imran Khan ya wuce gona da iri wa sojoji, kana a yayin da daga bisani ya amince da mukamin wanda sojojin ke so, koma baya ne a gare shi ta ko ina,” ya ce.

Sojojin da Mista Khan duka sun musanta cewa akwai wata takun saƙa.

Rashin nasara karo na uku?

Akwai misalai biyu kacal a tarihin siyasar Pakistan lokacin da firaminista mai mulki ya fuskanci kuri’ar rashin amincewa, kuma a duka lokutan Benazir Bhutto, a shekarar 1989, da Shaukat Aziz, a shekarar 2006, suka samu nasara ba tare da wata wahala ba.

Gwamnati na bukatar hukuncin kotun kolin da ba zai kawai haramta wa ‘yan jami’iar PTI da suka bijire kada kuri’a ba a karkashin dokar sauya sheka, har ma da haramta musu zama ‘yan majalisar dokoki kacokan.

Har ila yau, firaminista da ministocinsa na wayancewa, tare da ganawa da aminasau suna bayyana musu karfin guiwar da suke da shi na samun galaba.

Uzair Younus ya yi amanna duk da Imran Khan ya rasa damarsa ta yarjewa aminansa, kana koda a ce ya tsallake rijiya da baya a wannan guguwar da ke neman tafiya da shi”, zai kasance cikin wani mawuyacin matsayi.

“Ina ganin dole ya gudanar da zabuka da wuri. Muddin ko ta yaya, ya tsallake, iya tsawon lokacin da zai shafe a kan mulki, zai kasance iya yawan matsin lambar da zai fuskanta nay a gyara tattalin arziki,” ya ce.

A ganin Abdul Basit shi ma, kusan babu alamar samun damar tsallakewar Mista Khan, kana cigabansa ma babu wata nasara idan ma ya samu ya tsallake.

“Rayuwa za ta kasance cikin matsi idan aka duba halin da ake ciki a yanzu, dokar za ta kasance wata babbar barazana, shi yasa na ke hangen zabuka nan na watanni shida ko bayan hakan,” ya ce.

Shin ‘yan adawa sun yi wani kyakkyawan shiri?

A yayin da abokan hamayyarsa ke da hankoron ganin sun tsige shi, Mista Khan zai ji cewa ya cancanci karin yabo kan abubuwan da yayi a karkashin mulkinsa.

Duk da kalubalen annobar korona, jam’iyar PTI ta yi aiki tukuru wajen tallafa wa talakawa, in ji masu sa ido.

Alkaluman annobar corona na kasar Pakistan sun kuma nuna cewa – kasa mai mutane miliyan 220 ta samu wadanda suka kamu da cutar miliayn daya da dubu dari biyar kana wadanda suka mutu 30,000; adadi mafi karanci idan aka kwatanta da mummunar yaduwar cutar a kasar Indiya makwabciyarta.

Ga mai sharhi Arifa Noor, amma kuma, muhimmin aikin gwamnati na kiwon lafiya na bai daya – da aka kaddamar a lardunan Khyber Pakhtunkhwa da Punjab – gagarumar nasara ce.

“Ta bangaren jan hankulan masu kada kuri’a a zabuka masu zuwa, wannan ka iya zama babban taken su.

Wasu mutane b lallai ne a ce sun fuskanci mummunan bala’in cutar corona ba, amma shiri irin wannan na kiwon lafiya ka iya yin kyakkyawan tasiri a yanzu da ma nan gaba,” ta bayyana.

Mene ne abin da ‘yan adawa za su iya samar wa idan suka samu suka tsige gwamnati a kasar da babu wani firaministan da ya taba kammala cikakken wa’adinsa na shekara biyar?

“Da alama ‘yan adawa na son sus amu wata dama ne,” in ji Arifa Noor.

“Abin takaici, a kasarmu, saboa dokokinmu na mika mulki ba a tsare suke ba, a ko wane lokaci duk wanda ke kan mulki, wadaanda ke waje kan yi tunanin yayi daidai su rushe gwamnatinsu.”

Abdul Basit ya yi amann cewa ‘yan adawa na da damaar tsige gwamnati amma ba su yi wani kyakkyawan tanadi ba game da abinda ka iya faruwa a gaba – babu kuma alama sun damu da haka ba.

“Pakistan na tunkarar rikicin siyasa na wani dogon lokaci, na akalla shekara daya da rabi,” in ji shi.

Uzair Younus shima yana ganin ‘yan adawa ba su da wani kyakkyawan shiri da ya wuce tsige Imran Khan.

“Za su dauki wani mataki marar ma’ana ala tilas, kuma wanda za su sha matukar wahala a siyasarsu, da zai kasance musu wani babban kalubale,” ya ce.

“Amma kuma, ko wanene ya samu galaba, ko shakka babu wadanda za su fi rasa was u ne ‘yan kasar Pakistan.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here