Ecuador: Fursunoni 116 ne Suka Rasa Rayukansu a Rikicin Gidan Kaso

 

Shugaban Ecuador, Guillermo Lasso, ya tabbatar da mutuwar fursunoni 116 a tarzomar da ta barke a gidan kaso da ke birnin Guayaquil da ke gabar teku a ranar Talata.

An yankewa da dama daga cikin fursunonin ko dai hannu ko kuma kafafu, a tarzoma mafi muni da aka taba yi a wani gidan kaso da ke kasar. Inda akai amfani da bindiga, da aduna da gurneti da aka hada a gida da sauran muggan makamai a lokacin yamutsin.

Tuni shugaba Lasso ya ayyana dokar ta baci a birnin, ya kara da shan alwashin daukar matakan da suka da ce domin tabbatar da hakan ba ta sake faruwa ba.

Da zuba miliyoyin daloli domin inganta rayuwa a gidan kason da wannan na daga cikin dalilan da ake yawan samun tashin hankali tsakanin fursunoni lamarin da ke kaiwa ga hasarar rayuwaka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here