Ministan Wutar Lantarki ya Roƙi Gafarar ‘Yan Najeriya Akan Rashin Samun Wutar Lantarki

 

Ministan wutar lantarki, Sale Mamman ya roƙi gafarar yan Najeriya sabida matsalar rashin wutar lantarki da yan Najeriya suka fuskanta kwanan nan.

Ministan ya dangata hakan da lalacewar tashoshin samar da wutar da kuma rabata, amma ya tabbatar da ma’aikatarsa na aiki tuƙuru wajen warware matsalar.

Mamman ya tabbatar ma yan Najeriya da cewa duk komai zai dawo dai-dai, zasu ga haske kamar yadda suka saba gani Mininistan wutar lantarki, injiniya Sale Mamman ya nemi gafarar yan Najeriya bisa tsaikon wutar lantarki da aka fuskanta a faɗin ƙasar nan.

A wani saƙo da ya fitar ranar Alhamis, Mamman yace yayi dana sanin irin matsanancin halin da rashin wutar ya haifar wa yan Najeriya.

Ministan yace matsalar ta farune daga tashoshin wutar lantarki waɗanda suke da alhakin raba wuyar ga yan Najeriya, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Mamman yace: “Nayi matuƙar dana sanin ƙarancin wutar lantarki a faɗin ƙasar nan, da kuma wahalhaƙun da hakan ya haifar.

Ina mai tabbatar ma yan uwana yan Najeriya cewa muna aiki tuƙuru wajen ganin komai yadawo yadda yake ko ma yawuce haka.”

“An samu matsalar ne saboda lalacewar da wasu tashoshin wutar lantarkin waɗanda suke aikin raba wutar.

Tashoshin da suka samu matsalar sun haɗa da: Sapele, Afam, Olonrunsogo, Omotosho, Ibom, Egbin, Alaoji da kuma Ihovbor.”

Mamman ya tabbatarma yan Najeriya cewa ma’aikatar wutar tana aiki tuƙuru don ganin an gyara dukkan matsalolin da ake fuskantar tashoshin samar da wutar lantarki da kuma matsalar man gas da sauransu.

Ya kuma ƙara jaddada aniyar ma’aikatar wutar lantarki na dawo da wutar da ake samarwa a farkon wannan shekarar wacce takai 5,600MW.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here