Gwamna Ganduje ya Kaddamar da Sababbin Babura 25 ga Hukumar Karota
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da sabbin babura a Kano na hukumar KAROTA.
Hukumar ta KAROTA ta ce wannan baburan za su taimakawa jami’an hukumar wurin kama masu laifi da dakile masu shigo da haramtattaun kaya Kano.
Baffa Dan’agundi, shugaban KAROTA, ya ce da kudaden da aka samu bayan korar jami’an bogi aka siya baburan Gwamna Abdullahi Ganduje na jahar Kano ya kaddamar da babura na musamman guda 25 da hukumar rage cinskoso na jahar, KAROTA, ta siyo domin dakile cinkoso a jahar, Daily Trust ta ruwaito.
Da ya ke kaddamar da baburan a ranar Lahadi a Kano, Ganduje ya za a yi amfani da babburan ne somin tabbatar da cewa masu ababen hawa sun bi doka a kasa.
Read Also:
Ya ce baburan za su bawa jami’an KAROTA damar rasta wurare cikin gagawa domin sanya ido kan yadda masu saba dokokin tuki da gano masu shigo da haramtattun ababe zuwa jahar.
Gwamnan ya bukaci jami’an na KAROTA su zage damtse a kokarinsu na kula da cinkoson ababen hawa da kama masu saba doka.
Ya kuma bukaci su tabbatar an rika kama wadanda ke shigowa da haramtattun ababe zuwa jahar.
Ganduje ya yabawa shugaban KAROTA, Baffa Dan’agundi saboda bullo da wannan sabuwar tsarin.
Tunda farko, Dan’agundi ya ce an siyo baburan ne da kudaden da aka samu bayan korar ma’aikatan bogi a hukumar.
“Wasu lokutan, muna ganin abubuwa da dama suna faruwa, muna ganin miyagu suna daukan haramtattun abubuwa cikin motocci amma babu motoccin da za mu bi su zuwa wurin da za su tafi mu kama su.
“Amma, da wannan sabbin baburan, za mu iya kama masu laifi da dama,” Dan’agundi ya bawa gwamnan tabbaci.