Ɓangaren Gwamna Ganduje ya yi nasara a kotun ɗaukaka ƙara Kan Rikicin APC a Kano
Ɓangaren Gwamna Abudllahi Umar Ganduje ya yi nasara a ƙarar da ya shigar yana ƙalubalantar nasarar da wata kotun ta bai wa ɓangaren tshohon Gwamna Ibrahim Shekarau a rikicin jam’iyyar APC mai mulkin Jahar Kano.
A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce hukuncin da Babbar Kotun Abuja ta yi ba daidai ba ne sannan ta tabbatar da cewa shugabannin da ɓangaren Ganduje ya zaɓa su ne halastattu.
Read Also:
Hukuncin kotun na yau ya bai wa ɓangaren Ganduje nasara a duka ɓangarori ukun da suka ɗaukaka ƙarar a kan su, kamar yadda Barista Abdullahi Adamu Fagge ya shaida BBC Hausa – ɗaya daga cikin lauyoyin ɓangaren gwamna.
Tun da farko ɓangaren da Shekarau ke jagoranta ya shigar da uwar jam’iyyar ƙara da kwamatin shugbancinta na ƙasa da kuma sakatarenta a ɓangare ɗaya, sannan suka shigar da shugabancin APC na Kano a ɗaya ɓangaren, da kuma kwamatin da ya shirya zaɓen shugabancin jam’iyyar a Kano a wani ɓangaren daban.