Majalisar Harkokin Musulunci a Jahar Adamawa ta Haramta Dukkanin Bukukuwa da Ake yi Kafin da Kuma Bayan ɗaurin Aure

 

Majalisar harkokin addinin Musulunci a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta ce ta haramta dukkanin bukukuwa da ake yi kafin da kuma bayan ɗaurin aure a ƙaramar hukumar ne don ƙoƙrin samar da iyali na gari.

A baya-bayan nan ne aka ɗauki wannan a ƙaramar hukumar, wanda shugaban majalisar Ahmadu Liman Aminu ya ce an yi hakan ne domin samar wa matasa masu niyyar aure sauƙi da kuma samar da zuri’a ta gari ga matasa da ke auren.

Daga yanzu dai irin waɗannan kaɗe-kaɗe da a baya aka saba yi yayin bukukuwan aure sun zo ƙarshe, amma fa idan matakin dakatar da su ɗin ya fara aiki kamar yadda majalisar harkokin addinin Musulunci ta karamar hukumar Mayo Belwa take buƙata.

Malam Ahmadu Liman Aminu ya bayyana wa BBC dalilin daukar wannan matakin na dakatar da bukukuwa da aka saba yi kafun da kuma bayan aure.

“Saboda ganin wahalhalun da al’ummarmu suke sha a yayin waɗannan bukukuwa na aure da kuma yawan matasa da ke jibge da ba su yi aure ba, saboda dokokin da ya kamata a bi su a yayin ɗaura auren ma an bar su.

“Waɗannan dalilai ne suka sa ake haifar yaran da ba da tarbiyya waɗanda ke zame mana tashin hankali a ƙasa.

To ko waɗanne irin bukukuwa ne aka haramta?

An haramta tarukan liyafa irin su Cocktail Party da Ƙauyawa Day da Luncheon da Fulani Day da Budar Kai da ake gauraya tsakanin maza da mata.

Ta yaya za su tabbatar da an bi dokar?

Malam Ahmadu ya ce matakin da za su ɗauka a kan wanda duk ya ƙi bin dokar shi ne a ƙaurace wa mutum.

“Idan ka ƙi bin dokar to matakin da muka ɗauka na ƙaurace maka ne, idan za ka yi ɗaurin aure ko suna duk ba za ka ganmu ba.

“Ko rasuwa aka yi maka za mu ƙaurace ba za a je jana’izarka, wannan shi ne kawai matakin da muka ɗauka.”

Wasu ƙarin matakan da aka ɗauka

Har’ilayau majalisar ta kuma ƙayyade kayan aure zuwa akwati biyu kacal da za su ƙunshi atamfa bakwai da takalma uku da hijabai uku da gyale uku da da ƴan kunne uku da warworo uku da kayan kwalliya iya gwargwado.

Majalisar ta haramta karɓar ko wane irin kuɗi idan ba na sadaki ba, sannan ta hana yin kayan uwa da na uba da na dangi.

Majalisar ta kuma kafa wata cibiya da za ta riƙa yi wa waɗanda ke da niyyar aure lakca kan hakkokin da suka rataya a wuyansu.

Me masu niyyar aure ke cewa?

Salihu Adamu na BBC ya tattauna da wasu da ke sa ran zama ango da amarya a ƙarshen wannan makon kan yadda suka ji da wannan matakin.

Wani da muka sakaya sunansa ya ce: “Idan ka ce za a ka yi biki sai ka duba, za ka ɗauko hayar mai kiɗa da rumfuna wataƙila ma sai a gama bikin ba ka samu kuɗin da za ka biya waɗannan abubuwa ba.

“Don haka ni kam abin ya zo min yadda nake buƙata.

Ita ma wata mai shirin zama amarya ta ce “matakin da aka ɗauka ya yi kyau, dama bidi’o’in ba su da wani amfani.”

Da Salihu ya tambaye ta ko yaya za ta yi da ƙawayenta da suka shirya wataƙila don raƙashewa a bikin?

Sai ta ce: “Na gaya musu ni dama ba na waɗannan abubuwa.”

Wannan matakin na zuwa ne shekara ɗaya bayan da ƙaramar hukumar Gumel da ke jihar Jigawa ta dauki makamancinsa inda ta ƙayyade naira 100,000 a matsayin kuɗin kayan lefe.

Sau da dama dai malaman addinin Islama na nuna buƙatar soke wasu bukukuwa da ake yi yayin aure musamman waɗanda suke ganin sun saɓawa koyarwar addinin Musulunci da kuma ƙara wa aure tsada lamarin da suka ce na tilastawa wasu matasa shafe tsawon lokaci ba tare da yin aure ba.

To sai dai kuma irin wadannan matakan basu cika tasiri ba kasancewar a matakin kananan hukumomi ake sanyasu sannan babu wasu hukumomi dake tabbatar da sai mutane sun bi irin wadannan matakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here