Kotun Shari’ar Musulunci a Kasar Afghanistan ta sa an Jefe Mace da Namiji Kan Aikata Zina

 

Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zama a arewa maso gabas na Badakhashan a kasar Afghanistan ta sa an jifa kan wasu mace da namiji.

Mace da namijin sun amsa laifi da ake zarginsu da shi a gaban kotu kan cewa har sau uku suna zina kuma an kawo shaidu adilai hudu.

Kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, an aiwatar da hukuncin jifansu har suka sheka lahira a bainar jama’a.

An jefe wani mutum da wata mata a lardin arewa maso gabashin Badakhshan dake kasar Afghanistan, saboda sun aikata zina. Ma’aikatan Taliban ne suka tabbatar da hakan a ranar Laraba.

Wani ma’aikacin Taliban a lardin ya bayyana wa dpa yadda aka jefe su a kotun shari’a.

Shari’a musulunci ba ta yarda musulmai maza da mata su sadu da juna in ba da aure ba.

Haka zalika, idan mijin aure yayi zina da matar aure, kuma aka samu shaidu hudu, za a jefe duka biyun.

“Da kansu sun amince da sun aikata zina, kuma sun yi hakan sau biyu zuwa uku,” a cewar ma’aikacin.

Muezuddin Ahmadi, wanda ke kula da bangaren labarai da al’adun lardin ya ce, ana cigaba da bincikar lamarin, sannan ya yi alkawarin daukar tsatsauran mataki a kan wadanda suka jagoranci jifar.

Duk da bada tabbacin da hukumar tayi na cewa za ta girmama hakkin bil’adama, kananan ma’aikatan su da yawa suna karbar tsauraran horarwa a cikin watannin nan.

Karamar jaridar Hasht-e- Subh ta rawaito yadda aka yi jifar a bainar jama’a a ranar Litinin a yankin Nasi dake lardin. An samu labarin yadda kwamandan Taliban ya bada umarnin, Vanguard ta rawaito.

An samu labarin yadda kwamandan Taliban ya bada umarnin, Vanguard ta rawaito.

Lamari irin wannan yayi kamari a fadin kasar tun lokacin da Taliban suka amshi mulki.

Ana hana dalibai mata da dama zuwa makaranta sakandare, kuma an hana mata da yawa koma wa bakin aikin su.

An tilasta mata su saka hijabi, sannan a hada su da muharramin su, idan za su yi tafiya mai nisa.

Ana bawa maza karfin gwuiwar tara gemu da sanya kayan gargajiya na Afghan, yayin zama a ofisoshin gwamnati, Vanguard ta rahoto hakan.

An haramta wake-wake a kafar sada zumuntar zamani.Wadanda suke suka game da irin takurawar, suna fuskantar hantara ko zaman gidan yari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here