Daga Yaseer Kallah

Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya bayyana cewa kowanne irin kuskure Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya aikata, bai kyautu gwamnatin jihar ta tsaurara hukunci a kanshi haka ba.

Sarki Ningi ya shawarci ‘yan siyasa da gwamnatoci da su dinga yin juriya da hakuri a gurin hukunta sarakunan da suka aikata wani kuskure.

Yake cewa: “Abin da ya fi muhimmanci a gurinmu shi ne mu bai wa dukkan bangarorin da abin ya shafa hakuri. Da farko, a gaskiya ba ma farin ciki da abin da ya faru a Kano. Na yarda na yi magana a kan wannan batun kawai saboda matsayina na daya daga cikin tsoffin sarakuna a Arewa; a kan karagar mulki da kuma shekaru.

“Ba ma musu a kan cewa mai yiwuwa sarkin ya aikata wani abu da ba daidai ba. Mutum ne shi, amma shawararmu ita ce, in akwai wata ketare iyaka a bangaren sarkin, bai kyautu matakin da za a dauka ya yi tsananin da har ya ketare shi ya shafi gaba dayan masarautar da mutanenta ba.

“Dole ‘yan siyasa da gwamnatoci su zamo masu juriya da hakuri a kan hukumomin gargajiya. Ya kuma kyautu su zamo masu sassauta hukunci tare da afuwa ga sarakunan da suka aikata wani abu da ba daidai ba. Kada su zamo masu matukar tsanani a kan hukumomin gargajiya kamar yadda muka gani a jihar Kano. A gurina, abin takaici ne abin da ya faru a Kano, kuma karshen abin tsammani.

“Tun zamanin mulkin mallaka, bayan samun ‘yancin kai da lokacin Sardauna, ba a taba cin zarafin hukumomin gargajiya ba kai-tsaye kamar a wadannan lokutan. Hukumar gargajiya na hade da tarihi da al’adar mutane. Daga lokacin da aka lalata hukumar gargajiya, gaba dayan tarihi da al’adar mutane za su baci.

“Ya Kamata Gwamnatin jihar Kano, Masarautar Kano da Majalisar Dokokin jihar Kano su hada kai; su aje ra’ayi a gefe domin tseratar da tarihinmu da al’adarmu mai matukar muhimmanci.”

The post Ganduje ya wuce gona da iri kan Sarkin Kano – Sarkin Ningi appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here