Gwamna Ganduje Tare da ‘Yan Majalisar Kano Sun Kai wa Bola Tinubu Ziyara a Kasar Landan

 

Bayan walimar kammala karatun ‘dansa, Ganduje ya leka wajen Bola Tinubu.

Asiwaju Tinubu ya dade yana jinya bayan yi masa tiyata a Landan.

Ganduje ya samu rakiyar ‘dansa tare da yan majalisar Kano

Landan – Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano ya shiga jerin manyan jiga-jigan siyasan da suka garzaya birnin Landan domin gaida jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

A watan Yuli ne jita-jita suka yi ta yawo cewa an kwantar da tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, a wani asibitin waje, za ayi masa aiki.

Mai magana da yawun bakin babban ‘dan siyasar, Tunde Rahman, ya kartaya wannan batu, yace Tinubu ya na kasar waje, amma ba jinya yake yi ba.

Ganduje tare da ‘dansa, Muhammad Umar, da kuma wasu yan majalisar dokokin jahar Kano suka kaiwa jagoran siyasan ziyara.

Legit Hausa ta ci karo da hotunan ziyarar da wani Abubakar Aminu Ibrahim ya daura a shafin Facebook.

 

 

nigerian news up date

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here