Harin Jirgin Kasa na Abuja-Kaduna: Na Gargadi Hukumomin Gwamnatin Tarayya Game da Yin Tafiye-Tafiyen Dare a jirgin – Gwamna El-Rufai
Bisa ga alamu ana yar nuna yatsa tsakanin hukumomin gwamnatin tarayya da na jiha game da harin da yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa a Kaduna.
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce a baya, ya gargadi hukumomin gwamnatin tarayya game da yin tafiye-tafiyen dare a jirgin.
A bangarensa, ministan sufuri na kasa, Chibuike Amaechi ya ce ya bukaci a samar da kayayyakin tsaro a baya.
Jihar Kaduna – Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya yi gargadin a dena yin tafiyar dare da jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja.
Read Also:
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana da wasu wadanda suka tsira daga harin da yan ta’adda suka kai wa jirgin kasan a ranar Litinin 28 ga watan Maris.
wata bidiyon da Television Continental ta wallafa, bayan sauraron wani fasinja, Malam El-Rufai ya ce:
“Ka sani ko, na fada wa ministan a dena tafiya da jirgin bayan karfe 5 na yamma. Na ce a dena amfani da jirgin na yamma. Domin mun san akwai yiwuwar a kai hari da dare.”
Chibuike Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Jihar Rivers shine ministan da ke kula da sufuri.
“Fasinjan da ya fada wa gwamnan cewa yana aiki da hukumar jiragen kasa na Najeriya, NRC, ya tabbatar da cewa yan ta’addan sun sace mutane da dama.”