Sadiya Umar Farouq: Gaskiyata ta Fito Kan Rabon Abinci na Tallafin Korona
Ministar Ma’aikatar Jinkai da Cigaban Al’umma da Kare Afkuwar Bala’i a Najeriya ta faɗa wa BBC cewa wawason da wasu suka yi a rumbunan kayan abinci a jihohin kasar
ya wanke ta da kuma Gwamnatin Tarayya daga zargin ɓoye kayan tallafin annobar korona.
Hajiya Sadiya Farouq ta ce sun bai wa gwamnonin jihohi umarnin rarraba kayan tun a lokacin da suka kai musu.
“Mu dai mun sauke nauyin da ke kanmu, shugaban ƙasa ya ba mu kayan abinci kuma mun kai wa gwamnonin jihohi,” a cewar Sadiyar Farouk.
Sai dai ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta ce kayan da aka sace ɗin ba na gwamnati ba ne, tallafin da ‘yan kasuwa suka bayar ne. Ita ma fadar shugaban ƙasa abin da ta ce kenan.
Yayin wata ziyarar aiki da take yi a Jihar Zamfara, ministar ta faɗa ranar Talata cewa da ma ta san gaskiya za ta yi halinta.
Ta ce: “Ni dai ina aiki ne tsakani da Allah domin sauke amanar da aka ɗaura mani kuma da ma ina cewa gaskiya za ta fito. To alhamdulillahi.”
A ƙarshen makon da ya gabata ne dubban matasa suka fara fasawa tare da yashe rumbunan abinci a jihohin Kaduna da Filato da Adamawa da Oyo da Kwara da kuma Abuja.
Daga cikin abubuwan da matasan suka kwashe har da motar noma ta tarakta da magunguna.
Read Also:
Kazalika, an wawashe gidajen wasu ‘yan siyasa. Masu wawason sun ɗebe kekunan ɗinki da babura a gidan Sanata Teslim Folarin, mai wakiltar Mazaɓar Oyo ta Tsakiya da ke Jihar Oyo. Shi ma tsohon Kakakin Majalisar Wakila Yakubu Dogara an yashe gidansa.
A wata hira da BBC a ranar Talata, ministar ta ce tan 70,000 na kayan abinci suka tura zuwa jihohi.
“Kayan abincin tan 70,000 muka tura zuwa jihohi da kuma mota 156 – ko makamancin haka – kusa da haka na shinkafa da sauran kayan masarufi,” in ji ta.
“Shinkafar da hukumar kwastam ta ba mu, duka jihohin Najeriya muka bai wa. Amma abincin hatsi, jiha 24 muka bai wa.”
Game da uzurin da wasu gwamnoni suka bayar cewa sun ajiye kayan ne da nufin ko annobar korona za ta sake ɓarkewa a karo na biyu, ministar ta ce wannan gwamnonin ya shafa.
“To ni dai na kai kayan abinci kuma muna da bayananmu domin ba cikin dare ake yin wannan abin ba. Wannan kuma su za a tambaya, ba ni ba.”
Ministar ta ce akwai yiwuwar su duba yadda za a sake bayar da tallafin ganin yadda aka daka wa wannan wawa.
‘Yan kasuwa da suka haɗa da bankuna da kamfanoni sun bai wa gwamnatin Najeriya gudummawar biliyoyin naira da kuma kayayyaki a matsayin tallafi da za a bai wa mutane domin rage musu raɗaɗin da dokar kullen annobar korona ta saka su ciki.
Ita ma Gwamnatin Tarayya ta fitar da tan mai yawa daga nata rumbun ta hannun hukumar kwastam da ma’aikatar noma.
Ma’aikatar Sadiya Faruk ta jinƙai aka ɗaura wa alhakin rarraba kayan ga jiha 36 da Abuja, abin da ya jawo wasu ke kakkausar sukar ministar da ma’aikar tata cewa sun yi ƙwange.