Abuja: An Fara Wahalar Man Fetur

An fara fuskantar wahalar man fetur a Abuja babban birnin Najeriya.

Layukan motoci da sauran abubuwan hawa sun cika kusan kowanne gidan sayar da mai a Abuja, babban birnin kasar.

Tun a ranar Litinin mazauna Abuja suka fara fuskantar dogayen layukan a gidajen sayar da man fetur.

Amma kamfanin mai na NNPC ya ce matsalar ba wan abin fargaba ba ne domin akwai man yana nan wadace.

Kamfanin ya fadi a Twitter cewa “NNPC yana da litar fetir sama da biliyan biyu a ajiye da za a fitar domin samun wadatuwarsa.”

Wasu na ganin an fara shiga wahalar fetur din ne saboda dokar hana fita da aka kafa a wasu jihohi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here