Gawuna ya Ajiye Muƙaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwar Bankin Bayar da Lamunin Gidaje na Najeriya
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar gwamnan Jihar na jam’iyyar APC a 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwar bankin bayar da lamunin gidaje na Najeriya.
Sanarwar da tsohon mataimakin gwamnan ya fitar ta nuna cewa ajiye aikin zai fara ne daga gobe Talata, 31 ga Maris, 2026.
A cikin sanarwar, Gawuna ya ce “na ajiye aikin ne domin bin umarnin shugaban ƙasa da ya buƙaci duk mai riƙe da muƙamin siyasa kuma yake son yin takara, ya ajiye muƙami domin yin biyayya ga dokar zaɓe”.
Read Also:
A cikin wasiƙar ta Gawuna wadda ya tura wa Sakataren gwamnatin Tarayya, Gawuna ya nuna godiya ga shugaba Tinubu kan amincewa da shi da ya naɗa shi a matsayin shugaban Hukumar Gudanarwar bankin bayar da lamunin gidaje na Najeriya.
A makon da ya gabata ne aka yi ta raɗe-raɗin cewa tsohon mataimakin gwamnan, wanda ake wa kallon na hannun damar tsohon shugaban jam’iyyar APC ne ƙasa, Abdullahi Ganduje, cewa zai fice daga jam’iyyar APC, wadda ya yi takarar gwamna ƙarƙashinta a 2023.
A watan Janairun 2024 ne kotun ƙolin Najeriya ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano duk kuwa da cewa a watan Satumban 2023 kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen jihar Kano ta ayyana Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Tun farko hukumar zaɓen Najeriya ta ayyana Abba Kabir a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar ta Kano da aka yi a watan Maris ɗin 2023, inda ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya zo a matsayi na biyu da ƙuri’u 890,705.















