Ghana ta Ceto ‘Yan Najeriya 21 Daga Hannun Masu Safarar Mutane
Ghana ta mayar da ƴan Najeriya 21 gida, bayan ceto su daga hannun masu safarar mutane a Accra babban birnin kasar.
A ranar Talatar da ta gabata ne mahukuntan na Ghana suka ɗauki wannan mataki, inda suka ce daga cikin waɗanda aka ceton har da yara.
Read Also:
Akasarin su dai shekarunsu sun kama ne daga 15 zuwa 20.
Hukumar yaƙi da ayyukan zamba ta Ghana ta ce an ceto mutanen ne a watan Satumba, lokacin da jami’an tsaro suka kai samame a gidan da ake tsare da su, inda ake koya masu damfara ta intanet.
Haka nan hukumar ta ce bakwai daga ciki waɗanda aka kama na fuskantar tuhuma a kotu bisa zargin su da cin zarafi, da safarar bil’adama da kuma aikata manyan laifuka.