Ban ga ta Yadda Peter Obi Zai yi Nasara ba – Mukhtari Shagari

Tshohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto Mukhtari Shagari ya ce jam’iyyar Labour ta tuntuɓe shi domin tana son ya zama mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi.

Sai dai Alhaji Mukhtari a cikin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels ya ce ya ƙi amincewa da tayin saboda yana ganin cewar Peter Obi ba zai kai labari ba a zaɓen na shekara ta 2023.

A cewarsa “Ban ga ta yadda Peter Obi zai yi nasara ba.”

Ya ƙara da cewa “tabbas ana yawan ambato sunansa a kudu-maso-gabashin Najeriya haka nan kuma matasa na yawan ambaton sunansa a shafukan sada zumunta – wannan siyasa ce”.

“Amma gaskiyar lamari shi ne akwai manyan jam’iyyu biyu a ƙasar nan waɗanda suka mamaye komai – wato APC da PDP. Ina ganin idan har kana son ka zama shugaban ƙasa to dole ka zama a ɗaya daga cikin waɗannan jam’iyyu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here