Yayin da Gwamnatin Najeriya ta Kara Farashin Wutar Lantarki: Kasar Ghana Zasu Sha Wutar Lantarki Kyauta na Tsawon Watanni Uku

Al’ummar kasar Ghana za su mori lantarki kyauta na tsawon watanni uku.

Gwamnatin kasar ne ta bada wannan umurnin a matsayin tallafin rage radadin korona.

Sanarwar ta ce mutane masu karamin karfe da ke amfani da kilowat 0 – 50 na za su amfana.

Gwamnatin ƙasar Ghana za ta bayar da wutan lantarki na watanni uku kyauta masu ƙaramin ƙarfi a kasar tun daga watan Janairu zuwa Maris.

Rukunin waɗannan mutanen su ne waɗanda ba su amfani da wuta sosai akasin waɗanda ke da layukan wuta da yawa.

A cikin sanarwar ta suka fitar ranar Talata, Kwame Agyeman-Budu, shugaban kamfanin lantarki na Ghana ya ce wannan karamcin na cikin tallafin annobar korona ne da gwamnatin kasar ta bada.

Ya ce a ƙarƙashin shirin za a biya wa mutanen masu ƙaramin ƙarfi kudin wutansu na watanni uku daga watan Janairu zuwa Maris.

“Bisa umurnin shugaban kasar Ghana na kara wa’addin tallafin lantarki ga ‘yan Ghana, gwamnatin Ghana (GG) zata cigaba da daukan dawainiyar biyan kudin lantarki na (kwastomomin da ke amfani da kilowat 0-50) na tsawon watanni uku daga Janairu zuwa Maris din 2021,” a cewar Agyeman-Budu.

Sanarwar ta ce wadanda suka cika ka’idojin a biyu musu da ke amfani da mita za a saka musu lantarkin a cikin mitansu na watannin Janairu, Fabrairu da Maris.

Wadanda kuma ba su amfani da mita ta zamani za su saka katinsu a cikin mita kafin su tafi ofishin hukumar domin a saka musu unit din lantarkin a ciki a kowanne wata.

Har wa yau, hukumar ta tabbatarwa dukkan kwastomominsu da masu ruwa da tsaki cewa za ta zartar da dukkan umurnin da gwamnatin kasar ta bada. Ta shawarci duk masu wata matsala su ziyarci ofishin yankinsu don a warware musu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here