Kotun Jahar Kano ta Dakatar da Gina Shaguna a Kan Titunan Kasuwar Kwari

 

Babbar kotu dake zama a jahar Kano ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan kasuwar Kwari.

Kamar yadda mai shari’a S. B Namallam ya yanke a kotun, yace a dakata da gina shagunan har sai an kammala jin korafin.

Tun farko gwamnatin Kano ta bada fulotai domin gina shaguna tsakanin layin Ta’ambu da Bayajidda dake kasuwar Kwari.

Kano – Wata babbar kotu a Kano da ta samu shugabancin Mai shari’a S. B Namallam ta dakatar da gwamnatin jahar Kano daga gina shaguna a kan titunan kasuwar Kantin Kwari.

A cikin kwanakin nan ne gwamnatin jahar Kano ta bada fulotai a tsakiyar layikan Ta’ambu da Bayajidda dake kasuwar Kantin Kwari, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan al’amari babu shakka ya janyo cece-kuce tare da suka wanda jama’a suka dinga damuwa kan batun tsaro.

Su waye suka kai kara gaban kotu?

Wata kungiyar ‘yan kasuwa masu kishi da suka hada da: Shehu Bukar Makoda, Yushau Alaskan, Auwalu Buhari, Kabiru Isma’il, Salihu Baita da kuma gamayyar kungiyar kanana da matsakaitan ‘yan kasuwan Kano suka maka kamfanin RAZ, hukumar tsara birane da habaka ta jihar Kano tare da hukumar kula da filaye na jahar Kano a gaban kotu kan wannan cigaban.

Wanne hukunci alkali ya yanke?

Bayan sauraron lauyan masu kara, Abba Hikima, wanda ya gabatar da kokensu, kotun ta dakatar da wannan cigaban kan tituna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kotu ta bada umarnin wucin-gadi na dakatar da wanda ake kara na farko ko jami’anta da cigaba da gina shaguna a kan titunan Ta’ambu da Bayajidda a kasuwar Kantin Kwari dake Kano har dai an kammala shari’ar.

Umarnin ya haramtawa mai kare Kansa na farko daga shi ko wata kungiya daga bari a yi shagunan da zasu kare masu kara tare da take musu hakkinsu na walwala ta hanyar saka shaguna kan layikan Ta’ambu da Bayajidda na kasuwar Kantin Kwari dake Kano har sai an gama shari’a.

Ana umartar kowa da ya tsaya a matsayarsa har sai an kammala sauraro tare da hukunci kan wannan kara wacce za a yi shari’ar a ranar 19 ga watan Augustan 2021, umarnin yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here