Hukumar NDLEA ta Kama ‘Yan Ta’adda da Makamai a Jahar Katsina

 

Jami’an NDLEA sun cafke wasu bata-gari dauke da muggan makamai a jahar Katsina.

An kame su ne dauke muggan makamai da suka hada da AK-47 da sauran kayan laifi.

A halin yanzu an mika ‘yan ta’addan ga rundunar sojoji domin gudanar da bincike akansu.

Jami’an hukumar NDLEA sun cafke wasu mutane uku da ake zargi ‘yan bindiga ne; Adamu Shehu, Tukur Mohammed da Ibrahim Suleiman yayin da suke kai farmaki a jahar Katsina, tare da kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, da sauran abubuwa masu hadari.

An kama wani mai kera makamai, Celestine Chidiebere Christian, tare da babban bindiga kirar G3 tare da alburusai 78 (RLA) mai girman 7.62mm da kuma harsasai guda biyar a jahar Benue yayin da suke kokarin tura makamin da alburusan zuwa Jos, Jahar Filato.

An yi kamen da kwato makaman ne a wuraren binciken ababen hawa na NDLEA a jahohin biyu, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake magana yayin karbar makaman, Brig-Gen. Mohamed Buba Marwa (Mai ritaya), ya shaida cewa NDLEA za ta ci gaba da tallafawa kokarin da sauran hukumomin tsaro musamman rundunonin soji ke yi na dawo da doka da oda a fadin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a [email protected]! Ya ce:

“A bangarenmu NDLEA, za mu ci gaba da yin iya kokarinmu tare da manyan jami’ai masu himma don dakile amfani da muggan kwayoyi a kungiyoyin masu laifi ta hanyar hana fataucin wadannan abubuwan da ke kawar hankali.”

“Ta yin hakan, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ba da himma ga kokarin sauran hukumomin tsaro musamman sojojinmu a kokarin dawo da tsaro da kiyaye doka da oda a duk sassan kasar nan.”

A wane yanki aka kame ‘yan bindigan?

A cewarsa, jami’an NDLEA da ke sintiri a ranar Alhamis 5 ga Agusta, 2021 sun kama ‘yan bindigar uku a karamar hukumar Malumfashi ta Katsina.

An bayyana cewa wadanda ake zargin suna kan hanyarsu daga karamar hukumar Igabi ta Kaduna ne zuwa karamar hukumar Kankara a Katsina.

Marwa ya ce an kwato motar Toyota Corolla mai lamba Kaduna TRK 149 AE, bindigogi AK-47 guda uku da alburusai, layu iri -iri, zobba, tsabar kudi da sauran kayayyaki.

Ya kuma ce tuni ya ba da umurnin a mika wadanda ake zargi ga rundunar soji da ke Katsina domin ci gaba da bincike.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here