Gini Mai Hawa 20 ya Ruguje Kan Jama’a a Jihar Delta
Mutane da dama sun samu raunuka yayin da wani gini mai hawa 20 ya kife a Asaba jihar Delta da yammacin Alhamis.
Ganau sun bayyana cewa lamarin ya faru ba zato ba tsammani yayin da ma’aikata ke ci gaba da aikin ginin.
Kwamishininan sabunta birane na gwamnatin jihar Delta ya ce sun fara gudanar da bincike don gano ainihin abinda ya faru.
Delta – Wani ginin bene mai hawa 20 da ake aikin ginawa ya ruguje a Asaba, babban birnin jihar Delta, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
A cewar wani ganau da ibtila’in ya auku a kan idonsa, lamarin ya yi sanadin raunata mutane kusan takwas ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba,2023.
Ginin otal ɗin na biliyoyin Naira da ke daura da Delta Mall ya ruguje ne da yammacin ranar Alhamis yayin da ma’aikata ke tsaka da aiki.
Read Also:
An tattaro cewa ginin otal ɗin mallakin hamshakin attajirin dan kasuwa ne kuma wanda ya kafa kamfanin RainOil Group, Cif Gabriel Ogbechie.
Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Delta da jami’an tsaro sun kewaye wurin da lamarin ya faru a halin yanzu, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Mutun nawa rushewar ginin ta shafa?
Wata shaidar gani da ido ta ce ita da wasu da ke kasuwanci a kusa da wurin sun yi mamakin yadda kwatsam suka ji kara yayin da ma’aikatan ke tsaka da aikin ginin.
Matar, wacce ta bayyana sunanta da, Onyinye Okei, ta ce kusan ma’aikata Takwas suka samu raunuka kuma tuni abokan aikinsu suka garzaya da su Asibiti.
Me ya haddasa rugujewar ginin?
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala duba ginin da ya ruguje, kwamishinan sabunta biranen jihar, Mista Michael Anoka, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon rashin ingancin ginin.
Anoka, wanda ya tabbatar babu wanda ya mutu, ya ce:
“Muna kan aikin bincike don gano musabbabin faruwar lamarin kuma gwamnati ta fara daukar matakai kamar yadda kuke gani an rufe wurin. Bayan mun gama bincike, zamu faɗi rahoton abinda muka gano.”