Gobara ta Tashi a Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Kebbi

 

Gobarar tsakar dare ta kama a kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (TCN) da ke Birnin Kebbi.

Lamarin ya haddasa rudani a tsakanin mazauna kauyen Mechanic da ke Birnin Kebbi.

Legit.ng ta gano bidiyoyi a soshiyal midiya wanda ke nuna yadda gobarar ta shafi manyan kayan aiki na kamfanin raba wutar.

Birnin Kebbi, Jihar Kebbi – Kwana daya bayan gobara ta tashi a tashar wutar lantarki na Kainji da ke jihar Neja wanda ya yi sanadiyar daukewar wuta a fadin kasar, kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (TCN) da ke jihar Kebbi ya kama da wuta.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, har yanzu ba a san musababbin tashin gobarar ba.

Gobara ta tashi a kamfanin samar da wutar lantarki na Kebbi

Wasu mazauna yankin da kamfanin yake a bayan Mechanic Village da ke garin Birnin Kebbi sun ce sun ji karar fashewar abu sai kuma wuta da hayaki ya biyo baya daga wani sashi na kamfanin samar da wutar da misalin karfe 12:32 na dare.

Deeni Jibo, mai daukar hoton mataimakin gwamnan jihar Kebbi, ya ce bai taba ganin irin haka ba a rayuwarsa.Ya roki Allah ya kare wadanda ke cikin garin.

Kamfanin samar da wutar lantarkin shine ke raba wuta zuwa Kebbi, Sokoto da Zamfara da kuma Jamhuriyar Nijar, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

wanda shi ne mai daukar hoto na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin. Sai dai ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba.

Bayan daukar lokaci, an sake dauke wutar lantarki a fadin Najeriya baki daya A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa an dauke wutar lantarki gaba daya a fadin Najeriya.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis 14 ga watan Satumba a gaba daya fadin kasar.

Hakan ya faru ne makonni kadan da Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya cika shekara daya ba tare da an samu daukewar wutar gaba daya ba a kasar.

Sai dai kuma daga bisani Kamfanin Samar da Wutar Lantarki a Najeriya (TRCN) ta sanar da gyara wutar lantarki da ta baci.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com