Gobara: Mutane da Dama Sun Mutu a ƙasar Chadi

 

Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Deby, ya ce mutane da dama sun mutu wasu kuma sun jikkata bayan da wata gobara ta tashi a wani rumbun ajiyar makaman soji da ke N’Djamena, babban birnin ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Deby ya ce gobarar ta janyo ɓarna ga rayuka da kuma dukiya.

Ya yi alƙawarin ƙaddamar da bincike kan musabbabin tashin gobarar.

Mai magana da yawun gwamnati Kalamallah Abderaman, ya ce gobarar ta haifar da fashe-fashe.

Shaidu sun ce. sararin samaniya ya rikiɗe zuwa ja da baƙi, yayin da harsasan da aka ajiye ke tarwatsa kansu a unguwar Goudji da ke arewacin babban birnin ƙasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here