Jahohin Arewa: Kungiyar Matasan Yankin Arewa ta Bayyana Goyan Bayanta Kan Toshe Layukan Sadarwa

 

Wata kungiyar matasan yankin arewa ta bayyana goyon bayanta bisa toshe layukan sadarwa a wasu jahohin arewa.

Kungiyar cikin sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabanta da sakatare ta ce matakin yasa sojoji na samun galaba.

Ƙungiyar ta ce toshe layukan sadarwar ya sa ƴan bindiga ba su iya samun bayanai game da ayyukan sojojin daga ƴan leken asirinsu.

Matasan arewa sun nuna goyon bayan su bisa matakin da wasu gwamnonin yankin suka ɗauka na toshe layukan sadarwa kmaar yadda Daily Trust ta rawaito.

Gwamatin tarayya ta ɗauki matakin tsaro a jahohi kamar Zamfara, Katsina, Sokoto da Kaduna da suka hada da toshe layukan waya, hana sayar da man fetur a jarka, hana cin kasuwanni don daƙile ƴan bindigan.

Sojoji na samun galaba don ‘yan bindiga ba su samun bayyanai

A sanarwar da ta fitar a ranar Talata, Kungiyar Northern Youths Democratic Network ta bayyana harin da sojoji ke ƙaddamarwa kan ƴan bindiga a arewa maso yamma da maso gabas a matsayin abin da ya dace.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Dauda Mathias da Yahaya Abdullahi, shugaban kungiyar da sakatare, ta ce matakin toshe layin yana taimakawa sojojin sosai.

Sanarwar ta ce matakin ya sa ƴan bindigan ba su iya sanin lokacin da sojojin za su far musu hakan yasa sojoji na samun galaba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here