Babu Yadda za a yi Wanda ya Goyi Bayan Shugaban Kasa Har Sau Biyu, a Yau ya Zama Makiyinsa – Garba Shehu ga Mbaka
Malam Garba Shehu ya fallasa dalilin da yasa Mbaka ya bukaci shugaban kasa yayi murabus a kan rashin tsaro da ya addabi kasar nan.
Shehu yace Mbaka ya kaiwa Buhari ‘yan kwangila uku har fadar shugaban kasan amma Buhari ya bukaci su bi hanyar da ta dace.
A cewar mai magana da yawun shugaban kasan, babu yadda za a yi wanda ya goyi bayan shugaban kasan har sau biyu, a yau ya zama makiyinsa.
Fadar shugaban kasa tace Ejike Mbaka, shugaban Adoration Ministry (AMEN), ya taba kawai shugaban kasa ‘yan kwangila uku amma aka dakatar da shi.
Read Also:
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, yace Mbaka ya makance da har ya bukaci shugaban kasa ya yi murabus sakamakon tsanantar matsalar tsaro a kasar nan.
A wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a, Shehu yace akwai matukar abun mamaki ta yadda wanda ya goyi bayan shugaban kasan har sau biyu a yau ya sauya ya koma yana neman yayi murabus ko a tsige shi.
“Ga dalla-dalla: Mbaka ya bukaci ganawa da shugaban kasa amma kuma sai ya zo tare da ‘yan kwangila uku.
Shugaban kasan ya barsu sun ganshi amma abun mamaki sai Mbaka ya bukaci a basu kwangila domin biyansa goyon bayan da ya nunawa Buhari.
“Duk wanda ya san shugaban kasa Buhari ya san shi da rashin son karya dokoki ballantana a mu’amala da ‘yan kwangila.
Ya bukaci hukumomin da suka dace su duba lamarin kamar yadda doka ta tsara,” yace.