Greenfield: Tsohon Sanatan Jahar Kaduna, Shehu Sani ya yi Kira ga Gwamnatin Jahar da ta Ceto Daliban Dake Hannun ‘Yan Bindiga

 

 

Tsohon sanatan jahar Kaduna, Shehu Sani, ya ce ba daidai bane yadda gwamnatin jahar Kaduna ta nuna halin ko in kula ga daliban dake hannun ‘yan bindiga.

Shehu Sani yace in har akwai wata hanya da ta wuce sasanci ko biyan kudin fansa, toh gwamnati ta gaggauta bi don kubutar da daliban.

A cewarsa, ba zai yuwu a zuba ido ba har sai ‘yan bindiga sun watso mana gawawwakin ‘ya’yanmu 17 dake hannunsu ba.

Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna, yace akwai matukar hatsari abinda gwamnatin take yi na nuna halin ko in kula a kan garkuwa da ‘yan jami’ar Greenfield da aka yi.

Sama da dalibai 20 ne aka sace daga jami’a mai zaman kanta yayin da ‘yan bindiga suka kutsa makarantar a ranar 18 ga watan Afirilu.

Wadanda suka sace daliban sun bukaci kudi har naira miliyan 800 amma sai suka kashe biyar daga cikin daliban bayan an kasa biya masu bukatarsu.

A ranar Litinin, ‘yan bindigan sun ja kunne cewa zasu kashe ragowan daliban 17 dake hannunsu matukar ba a biya su kudi har miliyan dari ba tare da siya masu babura 10 zuwa ranar Talata.

Amma gwamnatin jahar Kaduna ta jaddada cewa ba zata taba sasanci ko bayar da kudin fansa ga ‘yan bindiga ba.

A yayin martani ga wannan ikirarin, Sani yace bai kamata a duba wannan barazanar ‘yan bindigan ba a banza. Ya tambaya gwamnatin jahar dalilinta na kin ceto daliban tunda ta ce ba za ta yi sasanci ko biyan kudin fansa ba.

“Idan biyan kudin fansa ba mafita bace, me yasa har yanzu jami’an tsaronmu suka kasa gano inda daliban suke balle a ceto su. Yin shiru akwai matukar hatsari,” Sani yace.

“Idan jama’a basu iya yi wa kansu komai kuma gwamnati bata iya masu komai, hakan na nuna cewa babu abinda za a iya. “Ba za mu iya jiran sai ‘yan bindigan sun watso mana gawawwakin ‘ya’yanmu 17 kofar gida ba. Ba zamu cigaba da ikirarin muna azumin watan Ramadan ba amma muna kallo ana yanka yaranmu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here