Guguwa Mai ƙarfin Gaske na Daf da Afka wa Mozambique
Hukumomi a Mozambique na kafa matsugunai tare da shirye-shiryen kwashe mutane a yankunan da ke da hatsari a daidai lokacin da wata mahaukaciyar guguwa ke tinkarar ƙasar.
Guguwar mai ƙarfin gaske ta afka wa makwaɓciyar ƙasar Madagascar a ranar Talata, inda ta kashe mutane biyar, kuma ana sa ran za ta ƙara tsananta kafin ta nufi kudu da tsakiyar ƙasar ta Mozambique a ranar Juma’a.
Lardunan Sofala da Inhambane da Manica da Gaza ne suka fi fuskantar haɗarin, a cewar jami’ai.
Read Also:
Hukumar bayar da agaji ta ƙasar, ta yi gargaɗi wanda ke ba da damar kai agaji cikin sauri.
Tuni dai ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haifar da ambaliya a wasu sassan ƙasar, kuma hukumomi sun ce ƙarin ruwan sama daga guguwar na iya shafar mutane miliyan 1.75.
A Zimbabwe, jami’ai sun ce za su rufe makarantu ranar Juma’a a wuraren da abin ya shafa.
An kuma gargaɗi mutane game da tsallakawa koguna da suka cika da ruwa tare da gargaɗin masu haƙar ma’adinai da su guji shiga karkashin ƙasa.
Ana sa ran guguwar za ta kawo iska mai karfin gaske da ruwan sama a gabashi da kudanci da kuma tsakiyar ƙasar ta Zimbabwe.