Ba ni ne ɗan Takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a NNPP ba – Shekarau

 

Ga alama an shiga ruɗani game da takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP kasancewar bayanai na nuna cewar har yanzu sunan Sanatar Malam Ibrahim Shekarau ne a hukumar zaɓe ta INEC.

Wannan na zuwa ne duk da irin ƙokarin da bangaren NNPP din suka yi na ankarar da INEC ɗin tare da rubuta musu takardar cewa sun sauya sunan Malam Shekarau da na Sanata Rufa’i Sani Hanga.

A tattaunawarsa da BBC, Malam Ibrahim Shekarau ya ce shi da kansa ya rubuta wa INEC cewa a sauya sunansa saboda ya bar jam’iyyar, amma sai ta ce masa lokacin canza sunan ɗan takara ya wuce, sai dai, idan ɗan takara ne ya rasu.

Ya ce tuni ya bar jam’iyyar NNPP kuma ba ita yake wakilta ba, inda ya ce ko da ya ci zaɓe ba a cikinta yake ba.

Sanata Shekarau ya kuma ce ya kira wanda yake takarar kujerar ta sanata a jam’iyyar NNPP, inda ya ce masa ya dakatar da yakin neman zaɓe saboda ba sunan shi ne a jerin sunayen da hukumar zaɓe ta san da su ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here