Wani Gunki Mai Shekarau 600 ya Samu ‘Yanci

An sace gunkin Ife Terracota, na masarautar Ife, daga Najeriya a shekarar 2019.

A cewar ministan labarai, Lai Mohammed, ya ce an bi da gunkin ta cikin kasar Ghana kafin zuwa kasar Netherlands.

Jami’an hana fasa kwauri na kasar Netherlands ne suka kama gungumen gunkin filin jirgin sama na Schiphol.

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya karɓi gunkin da aka dawo da shi na Ife Terracotta daga takwaransa na Ma’aikatar harkokin ƙasashen waje, Mr Geoffrey Onyeama.

An dawo da gunkin ne a ƙarƙashin wata tawaga da ta samu rakiyar wakilin gwamnatin ƙasar Netherland a Najeriya, Mr Harry van Dijk.

Da yake karɓar gungin a ofishinsa na Abuja a ranar Alhamis, Alhaji Lai Mohammed, ya ce dawo da gunkin Ife Terracotta ya nuna irin gagarumin shirin gwamnatin Najeriya na dawo da tsofaffin kayyakinta na tarihi.

“Na samu farinciki da annushuwa bisa karɓar wannan tsohon tarihi na Ife Terracotta wanda ya kai aƙalla shekaru 600.”

“Na ma fi jindaɗi da ya kasance ƙoƙarin ƙasarmu na ganin an dawo da tsofaffin kayayyakin tarihi, wanda aka ƙaddamar watan Nuwambar bara na shekarar 2019, ya fara bada yabanya” a cewarsa.

Ministan ya ce gwamnati na iyakacin bakin ƙoƙarinta don ganin an dawo da tsofaffin kayyakin ƙasa masu daraja wanda kuɗi bazai iya siyansu ba.

“Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya jajurce don ganin an karɓo tsofaffin kayayyakin tarihi don bunƙasa harkokin yawon buɗe da sauransu, don samun ƙarin kuɗaɗen shiga da ayyuka ga matasa.

“Hanya ce ta kuɗaɗen shiga idan har duniya ta san da kayayyakin al’adunmu, a matsayin mamallakan kayan al’adu, hakan zai bamu damar cin moriyarsu.

“Amma hakan ba mai yiwuwa bane idan har mafi yawa daga cikin kayyakin na hannun gidajen tarihi da hannun mutane masu zaman kansu,wanda suke bayyana kayan al’adun a matsayin mallakinsu.”

a cewarsa.Alhaji Lai Mohammed, wanda ya bayyana dawowa da gunkin a matsayin somin taɓi, ya ce baya ga ɗimbin moriyar da za’a samu, waɗannan kayayyakin tarihi na nuni da irin kyawawan al’adunmu daban daban a faɗin ƙasa.

Ya ce anyi safarar Ife Terracotta daga Najeriya zuwa Ghana sannan aka shiga da shi Netherlands da takurdun ƙarya a shekarar 2019.

Ministan yace an samu nasarar kama gano shi bayan kiciɓus da gungun gunkin ya yi da jami’an hana fasaƙwauri na ƙasar Dutch a filin jirgi na Schiphol a kasar Netherlands.

An gayyaci Najeriya don tabbatar da zarginta akan ɗan fasaƙwaurin, inda ƙasar ta tabbatar da laifin nasa, wanda hakan yayi sanadiyyar dawo da gunkin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here