Zambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP
Hukumar da ke Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Najeriya Zagon ƙasa EFCC ta sake gurfanar da Mamman Ali, ɗa ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasar Ahmadu Ali, bisa zargin zambar naira biliyan 2.2 na tallafin man fetur.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, ya ruwaito cewa an sake gurfanar da Mamman Ali tare da wani mutum mai suna Christian Taylor da kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd. a gaban wata kotu a birnin Legas.
An gurfanar da su ne bisa zarge-zagen laifuka 49 ciki har da haɗa baki, da yaudara da zamba cikin aminci, da yin ƙarya domin karɓar kuɗi da amfani da takardun bogi.
To sai dai mutanen sun musanta duka zarge-zargen da ake yi musu.
Lauyan hukumar EFCC Samuel Atteh, ya nemi kotun da ta sanya ranar sauraron ƙarar ta yadda zai gabatar da shaidunsa da za su tabbatar da zargin da hukumar ke yi wa mutanen.
Read Also:
To sai dai lauyan waɗanda ake zargin Kolade Obafemi ya nemi kotun da ta bayar da belin waɗanda yake karewa.
To amma lauyan EFCC ya ce abu mafi muhimmaci kan wannan shari’a shi ne waɗanda ake zargi su riƙa halartar kotun don fuskantar tuhumar da ake yi musu.
Daga ƙarshe alƙalin kotun ya bayar da umarnin cewa waɗanda ake zargin su ci gaba da kasancewa a hannaun hukumar EFCC har zuwa lokacin da za a gabatar da takardun neman belinsu a hukumance.
Alƙalin ya kuma ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu mai zuwa.
A ɗaya daga cikin zarge-zargen da hukumar EFCC ke yi wa mutanen, shi ne zargin haɗa baki don karɓar naira miliyan 750 daga gwamnatin tarayya, don karyar bai wa kamfanin mai na Nasaman Oil Services Ltd, ƙarƙashin asusun tallafa wa kamfanonin mai don shigo da litar mai 10,031,986, da kamfanin na Nasaman Oil Services Ltd, ya yi iƙirarin cewa ya saya daga kamfanin man Birtaniya na SEATAC Petroleum Ltd.