An Gurfanar da Wasu ‘Yan Najeriya a Gaban Kotu Akan Zanga-zangar Endsars
Wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam ya dauki matakin doka a kan wasu yan Najeriya 50.
A karar da ya shigar, mai fafutukar kare hakkin dan adam din ya yi bayanin cewa ya kai su kotu ne a kan rawar ganin da suka taka a zanga-zangar EndSARS.
Daga cikin wadanda aka yi kara akwai shahararrun mawaka, yan kwallon kafa, masu fafutukar kare yancin dan adam da kuma masu fada aji a soshiyal midiya An maka yan Najeriya hamsin a bangarori daban-daban da suka hada da mawaki David Adeleke, jagorar #BringBackourGirls, Aisha Yesufu da kuma Fasto Sam Adeyemi a gaban kotun majistare da ke Abuja.
An kai su kotu ne a kan rawar ganin da suka taka a zanga zangar EndSARS da aka yi kwanan nan.
A karar da wani mai fafutukar kare hakkin dan adam, Kenechukwu Okeke ya shigar, ya zargi wadanda ake karar da amfani da shafin Twitter wajen haifar da hargitsi da sunan zanga zangar EndSARS wanda daga bisani ya zama rikici.
Read Also:
Okeke ya ce aikin wadanda ake karar laifi ne da hukuncinsa yake a karkashin sashi na 97(2) na Penal Code Act, C53 dokar tarayyar Najeriya, 2004
“Bayan shigar da kara a kan wadanda suka bunkasa rikicin #EndSARS da karfe 1052hrs WAT, 09/11/2020, za mu tannatar da ganin cewa an hukuntasu saboda tsaro, da kuma kariyar jama’a.”
Legit.ng ta tattara jerin sunayen wadanda suka karfafa zanga zangar #EndSARS kamar yadda ta gani:
Aisha Yesufu
Oseni Etomi
Yemi Eberech Alade
David “Davido” Adeleke
Damini “burnaboy” Ogulu
Kanu Nwankwo
Kiki Mordi
Peter Okoye
Paul Okoye
Deji Adeyanju
Tiwa Savage
Feyikemi Abudu
Debo Adebayo
Folarin “Falz” Falana
Maryam “Taoma” Akpaokagi
Fakhriyyah Hasim
Oghenekaro Ibada Omu
Chbuzor Nelson
Ayo Sogunro
Pamilerin Adegoke
Chinedu Okoli
Micheal Collins Ajereh (Don Jazzy)
Yul Edochie
Ojabodu Ademola
Oduola Rinu
Tope Akinyode
Ogbeni Dipo
Small Doctor
Flavour Agbelese
Olamilekan
Layo Ogunbanwo
Kelvin Shekahu
Runtown
Ibrahim Wizkid Balogun
Damilola Odufuwa