Gwamnan Borno ya Fusata Kan Rundunar Sojoji

A ranar Litinin ne rahotanni suka bayyana cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun sace wasu matafiya.

Sun sace matafiyan ne a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno, ya nuna fushinsa akan kai harin.

Gwaman jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya nuna ɓacin ransa kan wani sabon hari da kungiyar yan ta’adda ta Boko Haram ta kai akan wasu matafiya a babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Gwamnan wanda yaya ziyarci Jakana, ɗaya daga cikin manyan garuruwan dake kan babbar hanyar Maiduguri-Damaturu, ya nuna matuƙar fushinsa kan sojojin bisa sace matafiyan da yan Boko Haram suka yi.

A cikin jawabin da ya fitar domin bayyana fushinsa, Zulum ya tambayi rundunar soji cewa ta ”yaya kuke sa ran zamu gamsu akan cewa zaku iya karemu, ku kawo karshen Boko Haram, idan har ba zaku iya tabbatar da tsaro a kan hanya mai nisan kilomita 20 ba?”.

Zulum ya ce, wannan babban abin takaici ne ganin yadda mafi yawan hare-hare na faruwa a dan tsakanin da nisansa bai wuce kilomita ashirin ba.

A bayanin gwamna Zulum, ya ce, “A gurare da dama na sha yaba kokarin sojoji domin karfafa gwuiwar kwamandoji da kuma dakarun da ke filin daga, saboda na san hakikanin yadda abin ya ke.

“Sai dai, sun ba ni kunya matuƙa gaya, duk da goyon bayan da muke ba su a nan Borno. Sojoji na nuna gazawa a yankin da bai fi kilomita ashirin ba tsakanin garin Auno da Jakana.” Cewar Zulum.

Zulum ya ƙara da cewa, “mafi yawan hare-hare na Boko Haram na cigaba da faruwa akan hanyar Maiduguri-Damaturu-Kano. Idan sojoji ba za su iya samar da tsaro a nisan da bai wuce kilomita ashirin ba, kenan mu daina sa ran za su ci galabar Boko Haram?”

Zulum ya ce, a wannan shekarar da muke shirin ban kwana da ita kaɗai, sama da matafiya 30 ne aka babbake su da wuta akan wannan hanyar ta Maiduguri-Damaturu-Kano ciki har da wata uwa mai shayarwa tare da jaririnta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here