Gwamnan Borno ya yi Godia ga Al’ummar jaharsa da Sojoji

Babagana Umara Zulum, gwamnan Jihar Borno ya karrama sojojin bataliya ta 151 da ke Bama a jihar Borno.

Gwamnan ya ce ya musu wannan karramawar ta musamman ne domin kungiyar Boko Haram bata taba galaba a kansu ba tun kafa su a Bama.

Zulum ya mika godiyar gwamatinsa da al’ummar Borno ga sojojin, ya kuma yi addu’ar Allah ya cigaba da kare su ya kawo zaman lafiya a jihar da kasa.

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum a ranar Talata ya ziyarci hedkwatan bataliya ta 151 na sojojin Najeriya da ke mahadar Banki da ke Bama inda ya yi musu albishir da kyauta ta musamman na kirsimeti.

Gwamnan ya bada kyautan da za a raba wa fiye da sojoji 700 da ke bataliyar ne saboda jajircewa da jarumtarsu kasancewa Boko Haram bata taba cin galaba a kansu ba tun kafa bataliyar.

Da isarsa, Zulum ya shiga ganawar sirri da kwamandan 21 armored brigade, Brig. Janar Waheed Shuaibu da kwamandan bataliya ta 151, Manjo A.A. Umar, daga baya kuma gwamnan ya yiwa sojojin jawabi.

“Saboda adalci, na kan karrama kowa dai dai kwazonsa. Mun samu kallubale a wasu wurare, sannan mun samu nasarori a wasu wurare kuma daya daga cikin inda aka samu nasara shine bataliya ta 151 domin Boko Haram basu taba cin galaba a kan ku tun kafa ku a Bama. Na zo nan ne a madadin gwamnati na da mutanen jihar Borno, don in muku godiya kamar yadda na saba yi a baya da kuma wasu bataliyoyin da ke jihar nan.

“Dukkanku kun nuna jarumta da kishin kasa. Muna godiya bisa sadaukar da kai da kuke yi duk da irin mawuyacin halin da kuke fuskanta a wurare daban daban. Ba abinda zai iya maye gurbin sadaukarwar da kuke yi. Muna godiya kuma muna addu’a Allah ya cigaba da kare sojojin mu da masu bada gudunmawa, Allah ya cigaba da baku nasara. Allah ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a Borno da Najeriya baki daya. Allah ya muku albarka,” in ji Zulum.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here