Gwamnan Borno ya Rantsar da Wasu Farfesoshi a Matsayin Shugabannin Kananan Hukumomi

 

Gwamnan jihar Borno, Fafesa Babagana Umara Zulum, ya ratsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi.

Daga cikin sabbin shugabannin kanananan hukumomin da aka rantsar akwai Farfesoshi biyu da wani mai digiri da digirgir.

Kazalika, Farfesa Zulum ya bayar da umarnin sakarwa kananan hukumomin kudadensu kamar yadda doka ta bukata.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jagoranci rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin kananan hukumomin jihar su 27 ciki har da Farfesoshi guda biyu da masu digirin digirgir.

Farfesoshi biyun sun hada da: Adamu Alooma, Farfesan ilimin banki da sha’anin kuɗi kuma shugaban tsangayar nazarin kimiyya a jami’a ta Maiduguri, wanda aka rantsar a matsayin shugaban karamar hukumar Damboa.

Sai kuma Ibrahim Bukar, Farfesan ilimi shima daga jami’ar ta Maiduguri, wanda aka rantsar a matsayin shugaban karamar.hukumar Gwoza.

Bikin rantsuwar ya gudana ne a dakin taro na Multipurpose dake gidan gwamnatin jihar Borno, inda gwamnan ya tunawa mahalarta taron da cewa jihar ta share sama da shekaru goma ba tare da gudanar da zaben kananun hukumomin jihar ba sakamakon rashin tsaro.

Bikin ya samu halartar manyan shugabannin jihar; tsohon gwamna Kashim Shettima, shugaban riƙon jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, sauran sun haɗa da mambobi na majalisar wakilai ta tarayya da ta jaha da sauran su.

Gwamnan ya taya sabbin zaɓaɓɓun shugabannin tare da kansilolinsu inda ya tunatar da su nauyin dake wuyansu wanda ya zama wajibi su sauke

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here