Gwamnan Ebonyi ya Sallami Wasu Hadimansa
Gwamnan Ebonyi ya sake rabuwa da wasu hadimansa bayan komawa APC.
Ya shahara da sallaman hadimansa idan ya fahimci ba sa aikinsu yadda ya bukata.
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya sallami hadimansa hudu kan zargin yiwa aikin da ya basu rikon sakainar kashi.
Sakataren gwamnan jihar, Kenneth Ugbala, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma kamfanin dillanci labarai, NAN, ta ruwaito ranar Asabar.
Read Also:
Wadanda aka sallame sun hada da Cletus Ogbonna, John Osi, Tochukwu Ali da Olachi Arua.
“Ana umurtan dukkan wadanda aka sallama su mika dukiyoyin gwamnati dake hannunsu ga SSG nan da ranar Litinin 23 ga Nuwamba,” jawabin yace.
Gwamnan, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ranar 20 ga Nuwamba, ya sallami hadimansa da dama da suka zo daga karamar hukumar Ohaukwu.
Wadanda sharan ya shafa sun hada da sukkan jagororin kananan hukumomi, hadimai, manyan hadimai, dss.