Zamfara: ‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Liman da Wasu Masallata, Sun Kashe Wasu

 

‘Yan bindiga sun kai hari masallacin Juma’a a kauyen Dutsin Gari a Kanoma Jihar Zamfara.

‘Yan bindigan sun kashe mutane biyar bayan sun bude wuta wadda hakan yasa liman ya datse sallar.

Sun yi garkuwa da liman da wasu mutum 40 amma sun sako limanin da wasu cikin mutanen a ranar Asabar.

‘Yan bindiga a ranar Juma’a sun afka masallacin Juma’a a kauyen Dutsin Gari a Kanoma, Jihar Zamfara sun yi awon gaba da liman da masallata kimanin guda 40.

Kauyen da ya yi suna saboda noman rake yana fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a baya bayan nan.

Kwararran majiyoyi a kauyen sun shaidawa Daily Nigerian cewa maharan da suka taho a kan babura fiye da 100 sun kashe masallata 5 sannan suka raunta da dama.

Majiyoyin sun ce harbe-harben da ‘yan bindigan da suka yi yayin da suka isa masallacin Juma’an ya janyo turereniya bayan liman ya yanke salla a raka’a na farko.

‘Yan bindigan sun yi awon gaba da limanin mai suna Mallam Yahaya da kimanin mutane 40 a kan babura suka shiga daji da su.

Wani mazaunin kauyen, Sani Kanoma ya shaidawa majiyar Legit.ng an sako limamin da wasu daga cikin masallatan daga baya a ranar Asabar.

Mista Kanoma ya ce bisa dukkan alamu ‘yan bindigan sun zo ne don sace manoman rake masu arziki sosai wadanda suka biya miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Zamfara, Mohammed Shehu ya ce zai bada cikaken bayani kan lamarin a ranar Lahadi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here