Gwamnan Jigawa ya yi Martani ga ‘Yan Adawa
Mohammad Badaru Abubakar, gwamnan jahar Jigawa, ya gargadi masu yi masa adawa da sukar manufofin gwamnatinsa.
Gwamna Badaru ya ce shiru-shiru ba tsoro bane ko rashin wayo, a saboda haka ba zai cigaba da jurar zaginsa ba.
Badaru na shan suka a cikin jam’iyyarsa ta APC da wasu jam’iyyun da suka goyi bayan gwamnan don samun nasararsa a zaben 2019.
Gwamna Mohammad Badaru Abubukar na jahar Jigawa, ya nuna matuƙar damuwarsa bisa yawan sukar da ya ke sha daga yan hamayya da ma wasu ‘yan jam’iyyarsa ta APC kan manufofin gwamnatinsa.
Read Also:
Da yake martani jim kaɗan bayan rantsar da shugabannin riƙo na jam’iyyar APC, gwamna Badaru ya ce, shuru-shuru a shugabanci fa ba tsoro ko rashin wayo ba ne, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Ya bayyana cewa yan siyasa a jihar Jigawa na amfani da saukin kansa suna zaginsa da sukar duk wata manufa mai kyau a jahar.
Gwamna Badaru na shan suka a cikin jam’iyyarsa ta APC da wasu jam’iyyun da suka goyi bayan gwamnan don samun nasararsa a zaben gwamna kuma suke ganin yanzu gwamnan na yin gwamnati ba da su ba.
Gwamnan ya fitar da gargadin cewa, “Rashin kiyaye wannan shawara, to kuwa mutum zai yi mummunar nadama, kamar yadda na gaya muku zan bar ofishina na koma harkar kasuwancina, idan jam’iyya ta fadi ku zargi kanku ni bani da asara.”