Ana Kokarin yi wa Shugaba Buhari Wani Shiri – Femi Adesina

Femi Adesina, mai magana da yawuun shugaban kasa, ya ce sun bankado wata makarkashiya da ake shiryawa shugaba Buhari.

A cewar Adesina, masu shirya wannan makarkashiya na shirin fara yada wasu labaran karya a ‘yan kwanaki masu zuwa.

Adesina ya ja hankalin ‘yan Nigeria su yi watsi da duk wata jita-jita da karya da za’a yada nan wani takaitaccen lokaci mai zuwa a gaba.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adeshina, ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya mai kama da juyin mulki da ake shiryawa shugaban ƙasa da cewa wai ba shi ne ke mulkin ƙasar nan ba.

Cikin bayanan nasa, Adeshina ya ce masu kulla wannan makarkashiya na shirin yaɗa wasu labaran ƙarya nan da yan kwanaki masu zuwa, kamar yadda TheCable ta rawaito.

“Muna janyo hankalin jama’a da su zama cikin shirin ganin wani gangami domin bata shugaban ƙasa da ofishinsa domin cimma wani buri na siyasa da ake kitsawa ta yanar gizo” Kamar yadda mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adeshina ya ce.

“Ana gab da fara gabatar da wannan shiri nan da yan kwanaki wanda ciki za’a nuna shugaba Buhari ba shine ke jagorantar ƙasar nan ba.”

Adeshina ya bayyana cewa ba komai ya janyo wannan abu ba face “yaƙi da cin hanci da rashawa da samar da tsaro tare da farfaɗo da tattalin arziki da yake ta yi, kuma wannan ba zai ɗauke hankalin wannan gwamnati daga abinda ta sa a gaba ba.”

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here