Gwamnan  Jahar Kano ya yi Martani Ga Masu Sukar Gwamnatinsa

 

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan Jahar Kano, ya ce masu sukar matakin da gwamnatinsa ta dauka kan wasu kamfanoni kauyawa ne.

Gwamnan Ganduje ya yi wannan furucin ne kan sauya ginin Triump da Daula Hotel zuwa wasu sabbin gine-gine.

Gwamnan ya ce wadanda ke suka abinda gwamnatinsa ta yi kauyawa ne kuma ba su yi binciken yadda zamani ke tafiya ba kafin tsoma baki kan batun.

Gwamnan Jihar Kano Abdulllahi Ganduje ya bayyana masu sukar yadda gwamnatinsa ta sarrafa wasu gine-gine ciki har da Daula Hotel a matsayin kauyawa marasa hangen nesa, Vanguard ta ruwaito.

Ya yi wannan furucin ne a yayin da ya ke duba Birnin Tattalin Arzikin Kano da aka kashe biliyoyin naira wurin ginawa da ke Dangwauro a kan Zaria road kusa da birnin Kano da yammacin Talata.

Da ya ke karin bayani a kan ayyukan gwamnatin Jihar Kano, Ganduje ya ce baya ga sayar da ginin Triump Newspapers da aka fi sani da Gidan Sa’adu Zungur, an sauya ginin zuwa kasuwar canjin kudade na zamani.

“Wadanda ke sukan mu ba su fahimci cewa aikin jarida na zamani baya bukatar babban gini domin wallafa jarida ba hakan yasa zamu mayar da ginin kasuwar canjin kudade na zamani.

“Masu canjin kudade na WAPA za su koma ginin kuma ‘yan kasuwan mu da dama za su amfana da wannan cigaban,” in ji gwamnan.

Ya kara da cewa wadanda ke sukarsa ba su fahimci yadda aikin jarida na zamani ke tafiya ba inda ya bukaci su rika bincike kafin tsoma bakinsu cikin batu.

“Wannan ya nuna sun jahilci yadda ake aikin jarida na zamani. Ya kamata a tunatar da mutane cewa gwamnatin da ta shude ne ta tilastawa jaridar Triump dena aiki kuma an dade da rufe kamfanin kafin mu zo mulki.

“Don haka su wane ke da laifi, wadanda suka kashe kamfani ko kuma wadanda suka fahimci muhimmancin ta suka dawo da shi,” ya tambaya.

Da ya ke magana game da wani kamfanin, Dauula Hotel, Ganduje ya ce kamfanin ya tsufa kuma baya tafiya da zamani. Don haka, zabin da ya rage wa gwamnati shine ta fara amfani da shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here