Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan ya yi wa Garba Shehu Wani Alkawari

 

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya sha wani alwashi tare da saka kudi $20,000.

Ya bukaci hadimin shugaban kasa, Malama Garba Shehu da ya kwana daya a Koshobe ko Kware shi kuwa zai ba shi $20,000.

Hadimin shugaban kasan ya zargi Omokri da wawuro kudin da ake hadawa don samun ‘yancin Leah Sharibu don bada wa, wanda yace baya so.

Reno Omokri, tsohon kakakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sha alwashin bai wa Garba Shehu kyautar $20,000 idan har ya kwana a Koshobe ko Kware.

Omokri ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.

Ya ce ya saka wannan kudin ne saboda Shehu ya ce Buhari ya tabbatar da cewa ya inganta tsaron kasar nan. Omokri ya nada Dele Momodu a matsayin shaida.

Koshebe da Kware wurare ne a jihohin Borno da Zamfara kuma an tabbatar da cewa suna cikin wurare da rashin tsaro ya tsananta kuma hare-haren ‘yan Boko Haram da ‘yan Bindiga ya yi kamari.

Omokri ya wallafa, “Garba Shehu ya ce janar Buhari ya inganta tsaro a Najeriya. Na yi alkawarin bai wa Garba Shehu $20,000 idan yayi kwana daya a Koshobe ko Kware. Dan jarida mai zaman kansa Dele Momodu ne zai zama shaida in har Garba ya amince zai je.”

A yayin martani ga wannan alwashin, Garba Shehu ya ce wannan kudin da Omokri ya saka yana daga cikin wadanda ya samu wurin gangamin bukatar a sako Leah Sharibu.

Shehu ya yi martani, “Idan har wannan kudin yana daga cikin wadanda ka karba domin gangamin sako Leah Sharibu, ba zan taba su ba. Adana $20,000.”

A yayin nuna amincewarsa, Dele Momodu ya ce, “matukar Garba Shehu ya karba wannan kalubalen kuma ya amince da tayin Reno Omokri, tabbas zan sanar da wanda yayi nasara.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here