Gwamnatin Najeriya na Son Hana Hawa Babura

Gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yuwuwar hana amfani da babura domin dakile ayyukan masu satar mutane da ‘yan ta’adda.

Ministan Shari’a kuma babban lauyan gwamnati Abubakar Malami shi ne ya sanar da haka a karshen taron majalisar tsaron kasar wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta yau Alhamis a Abuja.

A jawabin nasa ga manema labarai, ministan wanda ke tare da takwaransa na ma’aikatar cikin gida Rauf Aregbesola da kuma na ma’aikatar kula da harkokin ‘yan sanda Alhaji Maigari Dingyadi, ya ce, gwamnati na tunanin hana amfani da baburan da kuma aikin hakar ma’adanai.

Ya ce za ta yi hakan ne domin dakile hanyoyin da ‘yan ta’adda da masu satar mutane ke samun kudade da kuma jigilar kayayyakinsu.

Ministan ya bayyana cewa amfani da baburan na bai wa ‘yan ta’adda damar jigilar kudade da suke samu daga aikin hakar ma’adanai, su sayi makamai.

Sai dai kuma Malamin bai bayyana inda dokar za ta shafa ba, walau kasar baki Daya ko kuma wani bangare na kasar.

Da yake nasa jawabin ministan cikin gida Aregbesola ya ce duk da irin tarin bayanan sirrin da aka yi kafin harin da aka kai kan gidan yari na Kuje ranar 5 ga watan nan na Yuli, ‘yan ta’adda sun samu nasara saboda babu kudurin yakar su, kamar yadda ya ce.

Ya kara da cewana baw a Shugaba Buhari rahoton farko-farko na binciken da aka yi kan harin, tari da alkawarin cewa duk jami’in da aka samu da sakaci a aikinsa za a hukunta shi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here