An Ceto Jami’an ‘Yan Sanda 10 da ‘Yan Bindiga Suka yi Garkuwa da su a Jihar Kogi

 

Jami’an yan sandan da wasu miyagun yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kogi sun kubuta.

An ceto jami’an yan sandan su 10 a wuraren kauyen Jakura da ke Obajana ta jihar Kogi a ranar Laraba.

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa an kwashi jami’an nata wadanda aka kubutar ba tare da rauni ba zuwa asibitinta da ke Lokoja don basu cikakken kulawa.

Kogi – Jaridar Premium Times ta rahoto cewa an yi nasarar ceto jami’an yan sanda 10 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kogi.

An tattaro cewa an ceto jami’an tsaron ne a daren ranar Laraba, 20 ga watan Yuli.

An dai yi garkuwa da yan sandan ne a ranar Lahadi yayin da suke dawowa daga aikin zabe da suka yi a jihar Osun.

Labarin sakin nasu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumomin yan sandan suka fitar, jaridar Premium Times ta kuma rahoto.

Sanarwar ta ce:

“An ceto dukkanin jami’ai 10 da aka yi garkuwa da su ba tare da rauni ba.”

An ceto su ne a wuraren kauyen Jakura da ke Obajana kuma an dauke su zuwa asibitin yan sanda da ke Lokoja don samun kulawar likitoci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here