Maimakon N5bn: Gwamnatin Shugaba Tinubu ta Tura wa Jihohi N2bn
Gwamnatin shugaba Tinubu ta sakar wa kowace jiha a Najeriya Naira biliyan 2 maimakon biliyan N5 na rage radaɗin cire tallafin fetur.
Ministan kuɗi na tarayya, Wale Edun, ya ce FG ta yi haka ne domin kauce wa tashin farashin kayayyakin idan ta saki kuɗin baki ɗaya.
Ya ce shugaban ƙasa ya shirya tsamo yan Najeriya daga ƙangin talaucin da suka tsinci kansu ta hanyoyi daban-daban.
FCT Abuja -Gwamnatin tarayya ta tura wa kowace jiha Naira biliyan 2 ne kaɗai daga cikin Naira biliyan 5 da ta amince zata bai wa jihohi a matsayin tallafi domin rage tasirin cire tallafin man Fetur.
Gwamnatin karƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta sakar wa kowace jiha Naira biliyan 2 ne domin daƙile hauhawar farashin kayayyaki idan ta saki N5bn.
Read Also:
Ministan kuɗi na tarayya, Wale Edun, shi ne ya yi wannan bayanin yayin da yake zanta wa da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja ranar Jumu’a, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Mista Edun ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta lura da abinda ka iya biyo baya idan ta tura kuɗin baki ɗaya lokaci guda, bisa haka ta zaɓi raba sakin kuɗaɗen ga jihohi.
A rahoton Channels tv, Wale Edun ya ce kudaɗen da za a tura wa jihohin sun kasance na, “Tallafi da kuma rance ga gwamnatocin jihohi.”
Shugaba Tinubu ya lashi takobin bunƙasa zuba hannun jari
A jawabinsa, Ministan kuɗin ya ci gaba da cewa:
“Shugaban kasa Tinubu ya shirya samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Najeriya ta hanyar karfafa zuba jari da ke kara habaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi da rage talauci.”
Idan baku manta ba, shugaba Tinubu ya rantaar da ministocinsa a ranar 21 ga watan Agusta, 2023, inda ya ayyana Wale Edun a matsayin ministan kudi kuma kodinetan ma’aikatar tattalin arziki.